Ministan Lantarki Ya Nemi Afuwar ‘Yan Nijeriya Kan Ƙarancin Wuta, Ya Yi Alƙawarin Yin Gyara

[ad_1]

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya bai wa ‘yan Nijeriya haƙuri kan yawan ɗaukewar wuta da ake fama da shi, tare da alƙawarin cewa za a samu sauƙi nan ba da jimawa ba.

Ya ce matsalar ta shafi harkokin kasuwanci, makarantu da masana’antu, musamman a wannan lokaci na zafi.

  • Sin Ta Samu Ma’adanan Farin Karfe Marasa Nauyi Mafi Yawa Na Biyu A Duniya
  • Eid-el-Fitr:Kwankwaso Ya Buƙaci Magoya Bayansa Su Ci Gaba Da Jajircewa Kan Kyawawan Manufa

A cewarsa, babban abin da ya haddasa matsalar shi ne ƙarancin iskar gas da ake bai wa tashoshin samar da wuta, saboda bashin da ake bin masu samar da gas.

Adelabu ya kuma yi gargaɗin cewa rikicin Gabas ta Tsakiya na iya ƙara tsananta matsalar.

Ya bayyana cewa fannin wutar lantarki a Nijeriya ya dogara da gas ne, amma matsaloli kamar ƙarancin iskar gas, tsofaffin kayan aiki da matsalolin gyara na rage yawan wutar da ake samarwa.

Domin magance matsalar, ministan ya ba da shawarar ƙara amfani da makamashi kamar hasken rana da ruwa, ciki har da ƙananan tsarin samar da wuta (off-grid da mini-grid), domin rage nauyi a kan babban layin wuta.

Ya ce hakan zai taimaka wajen inganta wutar lantarki, rage kashe kuɗi, da kuma ƙara daidaita tsarin samar da wuta.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *