Ana Gudanar Da Taron Shekara-Shekara Na Dandalin Tattaunawa Na Boao

[ad_1]

A halin yanzu ana gudanar da taron dandalin tattaunawa na nahiyar Asiya wato BFA a takaice na shekara ta 2026 a garin Boao na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin, mai taken Kirkiro makoma ta bai daya: sabon yanayi, sabon zarafi, da sabon hadin gwiwa.

Taron na tsawon kwanaki hudu wanda ake sa ran kammala shi a ranar 27 ga wata, na kunshe da wasu sassan taruka da shawarwari sama da 50, inda wakilai daga bangarorin siyasa da kasuwanci da ilimi kimanin dubu 2 na kasashe sama da 60 ke halarta, don gudanar da tattaunawa mai zurfi kan batutuwan da suka shafi farfado da tattalin arzikin duniya, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da sauransu.

A gun taron manema labarai da aka yi yau da safe, sakatare-janar na dandalin BFA, Zhang Jun ya bayyana wasu muhimman abubuwan da ke tattare da taron na bana, da suka hada da: Na farko, yana jawo hankulan bangarori na sassan kasa da kasa. Na biyu, yana mayar da hankali kan samar da makoma mai haske. Na uku, yana da zummar tinkarar manyan matsaloli da dimbin kalubalen da shiyyarmu gami da duniya ke fuskanta a fannonin tattalin arziki da zaman rayuwar alumma.

Zhang Jun ya kara da cewa, bana shekara ce ta fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 na kasar Sin, kana ita ce shekara ta farko bayan fara aiwatar da matakan harajin kwastam na musamman a dukkanin fadin yankin cinikayya cikin yanci na Hainan, wato inda ake gudanar da taron BFA ke nan. Shi ya sa, makomar ci gaban kasar Sin shi ma ya zama wani muhimmin batun da ke jawo hankulan mahalarta taron. Zhang ya ce, taron zai samar wa mutane damar kara fahimtar lardin Hainan da ma kasar Sin baki daya, don neman cimma moriya tare.

Haka zalika, a gun taron manema labarai na yau, Zhang Jun ya gabatar da wasu muhimman rahotanni biyu, wadanda suka shafi makomar tattalin arzikin nahiyar Asiya da kokarin dinke shi baki daya, da kuma ci gaba mai dorewa ga nahiyar Asiya da ma duniya baki daya. (Murtala Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *