Sin Ta Yi Alkawarin Zurfafa Alakar Cinikayya Da Kenya

[ad_1]

Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng ya halarci taron dandalin kasuwanci tsakanin Sin da Kenya a Nairobi jiya Litinin, inda ya sake jaddada kudirin kasar Sin na fadada cinikayya da Kenya da kuma yankin Afirka baki daya.

Han ya ce a watan Afrilun bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Kenya William Ruto sun amince da daukaka dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu zuwa matsayin al’ummar kasar Sin da Kenya mai kyakkyawar makoma ta bai-daya a sabon zamani, lamarin da ya samar da alkiblar raya dangantakar ta dogon lokaci.

Kazalika, Han ya ce kasar Sin za ta ci gaba da jajircewa wajen fadada bude kofa ga kasashen waje, kuma za ta bayar da damammaki tare da cimma nasara tare da sauran kasashe, ciki har da kasar Kenya ta hanyar samun ci gaba mai bude kofa.

Kafin taron dai, Han ya tattauna da mataimakin shugaban kasar Kenya Kithure Kindiki. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *