Kotu ta ɗaure tsohon Akanta-Janar shekaru 72 kan badaƙalar N868m

[ad_1]



Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon muƙaddashin Akanta-Janar na Tarayya, Chukwunyere Nwabuoku, hukuncin ɗaurin shekaru 72 a gidan yari ba tare da zaɓin tara ba, bayan samunsa da laifin badaƙalar kuɗaɗe har naira miliyan 868.

Da yake yanke hukuncin a ranar Litinin, alƙalin kotun, Mai shari’a James Omotosho, ya bayyana cewa Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa, ta tabbatar da tuhume-tuhumen almundahanar kuɗaɗe har guda tara da ake yi masa ba tare da wata shakka ba.

Kotun ta same shi da laifi a dukkan tuhume-tuhumen guda tara, inda ta yanke masa hukuncin shekaru takwas kan kowace tuhuma—jimillar shekaru 72 ke nan—inda kotun ta umarci a zartar da hukuncin a lokaci guda.

Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa laifin da Nwabuoku ya aikata na karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin tsaro da harkokin soja a lokacin da yake Daraktan Kuɗi a Ma’aikatar Tsaro abin takaici ne matuƙa.

Kotun ta kuma tabbatar da cewa cikin shaidun da aka gabatar wanda ake tuhumar ya mayar da sama da Naira miliyan 200 daga cikin kuɗaɗen da aka sace yayin bincike, lamarin da ɓangaren masu kare shi ba su musanta ba.

Ana iya tuna cewa, an dai gurfanar da Nwabuoku ne a ranar 15 ga Janairu, 2025 kan tuhume-tuhume guda tara na na badaƙalar kuɗaɗe, a ƙarƙashin shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CR/240/2024 da EFCC ta gabatar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, ana zargin tsohon Akanta Janar ya aikata laifin ne tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021, lokacin da yake riƙe da muƙamin Daraktan Kudi da Asusun Ma’aikatar Tsaro.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *