Lesotho Tana Son Yin Aiki Da Kasar Sin Don Amfanad Da Jama’arsu Ta Hanyar Hadin Gwiwa
[ad_1]
Firaministan kasar Lesotho Sam Matekane, ya bayyana wa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin a kwanakin baya cewa, kasar Lesotho ta kiyaye yin hadin gwiwa tare da kasar Sin cikin dogon lokaci, da samun nasarori masu yawa, kuma kasar Lesotho tana son yin aiki tare da kasar Sin wajen sa-kaimi ga raya dangantakarsu da amfanad da jama’arsu baki daya.
Matekane ya bayyana cewa, a shekarun baya-baya nan, kasashen biyu sun yi hadin gwiwa da juna a fannonin ayyukan more rayuwa, da aikin noma, da ba da ilmi da sauransu, hakan ya samar da gudummawa wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma da kuma kyautata zaman rayuwar jama’a a kasar Lesotho. Hadin gwiwar dake tsakanin kasar Lesotho da kasar Sin ya kiyaye amfand da jama’ar kasar Lesotho.
Game da yanayin da ake ciki a kasashen duniya, Matekane ya bayyana cewa, kasar Lesotho ta kiyaye bin tunanin tabbatar da ikon mulkin kai da zama tare da sauran kasashe cikin lumana, kana ta nuna goyon baya ga shawarwari na guda 4 da kasar Sin ta gabatar. Kasar Sin babbar kasa ce dake daukar nauyin da ya rataya a wuyanta, kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali mai karko a duniya, kana kasar ta Lesotho tana fatan kasar Sin za ta ci gaba da bayar da karin gudummawa a nan gaba. (Zainab Zhang)
[ad_2]
Source link