Kano: Cikakken Dalilin Soke Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Kano ta soke ma’aikatar ilimi mai zurfi wadda ke karkashin kulawar mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam Gwarzo mutumin da ya ke fuskantar matsaloli masu yawa, ta hada da daya da ma’aikatar ilimi ta Jihar a matsayin tsarin ta na kawo gyara kan lamarin ilimi a Jihar.
Gwamna Abba Yusuf shi ne ya amince da yin hakan, a matsayin wani mataki na kawo gyara kan lamarin ilimi da kuma rage yawan kudaden na yadda ake tafiyar da Shugabanci a Jihar.
- Abincin Sallah
- Kuncin Rayuwa: Jam’iyyun Adawa Da Kungiyar Kwadago Sun Caccaki Tinubu
Wannan ci gaban an same shi ne ranar Lahadin da ta gabata daga bakin mai ba gwamnan shawara a kan harkokin yada labarai, Sunusi Bature.
Ta hakan ne ita ma’aikatar ilimi mai zurfi wadda shi mataimakin Gwamnan ke kulawa da ita, ta daina zama ma’aikata mai zama mai irin wancan aikin, da yanzu ma’ikatar ilimi ta kasance mai yin aikin da take yi.
A sabon tsarin kamar yadda gwamnatin ta bayyana, za’ a kirkiro wani sabon sashe ne na musamman da ya shahara kan lamurran ilimi mai zurfi,a cikin ma’aikatar ilimi, ya rika da harkokin ilimi mai zurfi a illahirin Jihar.
Kamar dai yadda bayanin ya nuna, Babban Sakatare ne zai jagoranci da kulawa da shi sabon sashen, da taimakon ma’aikatan da suke da ruwa da tsakin kan lamarin Mkarantun ilimi mai zurfi.
Hakanan kuma sauran Hukumomin da suke karkashin ma’aikatar ilimi mai zurfi, da suka hada da Hukumar bada taimakon kudade na yin karatu, yanzu za ta koma a, karkahin ma’aikatar ilimi.
Hakanan ma,duk Jami’oin Jihar da manyan Makarantu yanzu sabon sashen ne da aka hada da ma’aikatar ilimi zai rika kulawa da su.
Gwamnatin ta ce gyaran da aka yi ya na karkashin tsarin da ake son yi domin kawo gyara na zummar gyara bangaren ilimi, ta hanyar sake kawo gyara akan ayyukan da suka kasance daya, da bunkasa tsare- tsare ga dukkan bangarorin ilimi, da kuma tabbatar da ana tafiyar da su tsare- tsaren kamar yadda ya dace.
Gwamna Yusuf ya ce matakin an shirya shi ne domin a rage kudaden yadda ake tafiyar da ayyukan gwamnati da kuma inganta tsarin tafiyar da gaskiya, da kuma bunkasa a gaba daya inganci wajen tafiyar da tsarin ilimi a Jihar.
Ya tabbatar da tsarin tafiyar da gwamnatin sa lamarin zai kasance ne wajen maida hankali wajen aiuwatar da su tsare- tsaren wadanda za su farfado da martabar ilimi, domin hakan zaman tamkar wata fitila ce da za ta rika haskewa matasa abubuwan da suka dace su yi domin bunkasar Jihar baki daya.
Bugu da kari kuma, ya umarci Ofisoshin Sakataren gwamnatin Jihar da na Shugaban ma’aikata da cewar su tabbatar da duk an yi abubuwan da suka dace ayi da kuma tafiyar sabbin sassan wajen sake masu yadda za su kara inganta ayyukansu.
[ad_2]
Source link