Za mu ƙara ƙaimi wajen daƙile matsalar tsaro — Radda

[ad_1]



Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ƙara ɗaukar matakan da suka dace domin daƙile matsalar tsaro a faɗin jihar.

Radda ya bayyana haka ne bayan kammala sallar Eid-el-Fitr a garin Batagarawa, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Gwamnan ya kuma nuna alhininsa kan hare-haren ‘yan bindiga da suka auku a ƙauyukan Falale da Kadobe da ke ƙaramar hukumar Jibiya, tare da kira ga al’umma da su ƙara haɗa kai da juna.

Ya buƙaci musulmi da su ci gaba da yin addu’o’i domin samun zaman lafiya mai ɗorewa a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Radda ya halarci sallar ne bayan dawowarsa daga ƙasar Birtaniya, inda ya kasance cikin tawagar da ta yi rakiyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ziyarar aiki ta kwanaki biyu a ranar 18 da 19 ga watan nan.

A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da shagulgulan Sallah a sassan jihar cikin kwanciyar hankali.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *