Uromi: Shekara guda bayan kisan mafarauta, Gwamnatin Kano ta tallafa wa iyalansu

[ad_1]



Shekara guda bayan kisan wasu mafarauta a yankin Uromi na Jihar Edo, Gwamnatin Jihar Kano, ta tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma waɗanda suka tsira daga harin.

Gwamnatin ta raba kuɗi da kayan abinci ga waɗanda lamarin ya shafa.

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya ne, ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai Ƙaramar Hukumar Bunkure, inda aka tara iyalan mamatan da waɗanda suka jikkata.

Ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya bayar da umarnin raba tallafin bayan ya gano cewa ba a cika alƙawarin da aka ɗauka ba tun lokacin ziyarar ta’aziyya.

A cewarsa, kowane daga cikin iyalai 16 na waɗanda aka kashe ya samu Naira dubu ɗari uku (N300,000).

Waɗanda suka tsira sun samu Naira dubu ɗari biyu (N200,000) kowannensu.

Haka kuma, kowane ya samu buhunan shinkafa guda biyu.

Waiya, ya tuna cewa a baya, Gwamna Abba, ya ziyarci yankin tare da takwaransa na Jihar Edo, domin jajanta wa iyalan bayan harin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.

Ya ƙara da cewa yayin da Jihar Kano ta cika nata alƙawarin, Gwamnatin Jihar Edo ma ta tabbatar da cewa za ta biya diyyar nan ba da daɗewa ba.

“An riga an buɗe asusun banki domin iyalansu, kuma muna sa ran Gwamnatin Jihar Edo za ta turo kuɗaɗen nan ba da jimawa ba,” in ji shi.

Kwamishinan ya roƙi iyalan da su ci gaba da haƙuri, inda ya tabbatar musu da cewa gwamnatocin biyu na yin iyakacin ƙoƙarinsu domin tallafa musu da kuma tabbatar da adalci.

Ya bayyana lamarin a matsayin “babban rashi ga ƙasa” tare da yin addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu.

Haka kuma, Waiya, ya bayyana cewa kwamitin da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa ya yi aiki tare da hukumomin Jihar Edo domin magance matsalolin da suka taso.

Ya sake jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da tallafa wa waɗanda abin ya shafa da kuma nuna goyon baya ga iyalansu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *