Sallah: FRSC ta haramta wa ƙananan yara tuƙi a Gombe

[ad_1]



Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Gombe, ta gargaɗi ƙananan yara kan yin tuƙi, yayin bukukuwan Sallah.

Kwamandan hukumar a jihar, Samson Kaura, ya ce duk wanda bai kai shekara 18 ba bai kamata ya yi tuƙi ba, domin hakan na da haɗari sosai.

Ya bayyana cewa daga cikin abubuwan da ke haddasa haɗura akwai gudun wuce ƙima, lodi fiye da ƙima, tuƙin ganganci, da kuma amfani da waya ko ƙwayoyi yayin tuƙi.

Kaura, ya nuna damuwa kan yadda ake ganin ƙananan yara suna tuƙa motoci da babura a wasu sassan jihar, yana mai cewa hukumar ba za ta yarda da hakan ba.

Ya ce hukumar ta fara sintiri na musamman domin tsaro a lokacin bukukuwan Sallah, inda aka tura jami’ai a manyan hanyoyi domin tabbatar da zaman lafiya.

“Masu rai ne kaɗai ke yin biki, don haka a riƙa tuƙi a hankali tare da fifita tsaro,” in ji shi.

Haka kuma, ya gargaɗi iyaye da kada su bar ’ya’yansu ƙanana su riƙa tuƙi, domin hakan na jefa rayuka cikin hatsari.

FRSC ta kuma tura jami’ai sama da 620, tare da motoci 10 na sintiri, motoci huɗu na ɗaukar marasa lafiya, da kuma mota mai jan motoci domin taimakon gaggawa.

A ƙarshe, Kaura ya taya Musulmi murnar Sallah, yana mai cewa hukumar za ta ci gaba da ba da kariya da taimakon gaggawa a duk lokacin da ake buƙata.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *