Kotu Ta Yanke Hukuncin Shekara 15 Ga Wani Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi A Kano

[ad_1]

Hukumar NDLEA ta samu nasarar gurfanar da wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, Jonathan Nuhu, wanda wata Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 15 bisa samunsa da laifin mallakar tabar wiwi ba bisa ƙa’ida ba.

A wata sanarwa da kakakin hukumar a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari, ya fitar, ya ce Mai shari’a M.N. Yunusa ne ya yanke hukuncin a ranar 17 ga Maris, 2026, inda ya yankewa mutumin mai shekaru 45 ɗan asalin Jihar Filato hukuncin.

  • NDLEA Ta Kama Tsoho Da Yunƙurin Safarar Hodar Iblis A Filin Jirgin Sama Na Abuja
  • Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 9 A Wurin Shaƙatawa A Filato

Sanarwar ta ce jami’an NDLEA sun kama Jonathan ne a ranar 20 ga Yuli, 2023, a kusa da gadar Wudil a ƙaramar hukumar Wudil ta Jihar Kano, inda aka same shi da buhuna 116 na tabar wiwi.

An gurfanar da shi a gaban kotu, kuma bayan shari’a da bincike na tsawon shekaru uku, kotun ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari.

Hukumar ta kuma bayyana cewa Jonathan Nuhu ya taɓa samun irin wannan hukunci a Jihar Jigawa a shekarar 2021 kan laifi makamancin wannan, duk da cewa yana kan beli kafin a sake kama shi, inda ta jaddada ƙudirinta na ci gaba da cafke wa da gurfanar da masu aikata irin waɗannan laifuka.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *