Masanan Afirka: Shirin Shekaru Biyar-biyar Na Kasar Sin Karo Na 15 Ya Ba Da Sabbin Damammaki Na Ci Gaba Ga Afirka

[ad_1]

Shirin raya ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar na kasar Sin karo na 15 da aka amince da shi a kwanan nan, ya samar da damammakin da kasashen Afirka za su iya amfani da su yayin da suke bin hanyoyinsu na samun ci gaba, kamar yadda manazarta suka bayyana a wani taron kara wa juna sani da aka gudanar a Kampala jiya Talata.

Taron, wanda aka gudanar bisa taken “Dabarun daidaita sahu don samun wadata: Zurfafa alakar da ke tsakanin Sin da Uganda a cikin shirin shekaru biyar-biyar karo na 15,” ya samu halartar masu bincike, masana ilimi da kuma jami’an gwamnati. Cibiyar kwararrun masu nazari da ke sa-ido kan ci gaba, watau DWC da ke Uganda ce ta shirya taron.

Wani mai bincike na cibiyar DWC Arthur Atuha, ya bayyana cewa kasashe kamar Uganda za su iya cin gajiyar zurfafan fasahohin kimiyya da kirkire-kirkire na kasar Sin wajen sarrafa kayayyaki cikin hanzari domin kaiwa kasuwar kasar Sin.

Kazalika, shi ma wani mai bincike a cibiyar binciken kimiyyar dan Adam ta Afirka ta Kudu Vuyo Mjimba, ya bayyana cewa shirin na shekaru biyar-biyar na kasar Sin karo na 15 ya nuna muhimmancin yadda kasashen Afirka za su ci gaba da dagewa wajen ba da fifiko ga ci gaban kansu, maimakon dogaro da tsare-tsaren wasu daga waje.

Har ila yau a nasa bangaren, wani jami’in bincike a cibiyar DWC Joshua Kingdom, ya bayyana cewa kasar Sin ta riga ta aza harsashi a yankin Afirka domin zurfafa cudanyar kasuwanci a yayin da take habaka zamanantarwa da kuma samun ci gaba mai inganci a matakin koli. Ya kara da cewa, a karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, watau BRI a takaice, kasar Sin ta ba da goyon baya ga gina muhimman kayayyakin more rayuwa na makamashi da sufuri, wadanda za su iya taimaka wa kasashen Afirka wajen yin amfani da damammakin da suka samu.

Sannan, Mai fashin baki a fannin tattalin arziki dan asalin kasar Guinea-Bissau Afonso Gomes ya bayyana cewa, manufar da kasar Sin ta sanar ta yafe harajin fito kan hajojin kasashen Afirka 53 da ake shigarwa kasar Sin, za ta haifar da wani sabon mafari na yaukaka alakar Sin da kasashen nahiyar Afirka, kuma hakan zai kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Mr. Afonso Gomes ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawar baya bayan nan da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua.

Gomes ya ce, manufofin kasar Sin sun dace da aniyar kasar ta goyon bayan cudanyar mabambantan sassa, da zurfafa hadin gwiwa da kasashen Afirka. Ya ce hakan zai bude sabbin damammaki ga kasashen nahiyar Afirka na fitar da karin hajoji da aka karawa inganci, da samar da guraben ayyukan yi a gida da fadada kudaden shigarsu. Kazalika, manufar za ta taimakawa kasashen Afirka da damar rage fatara, da karfafa ikon nahiyar na cimma dogaro da kai ta fuskar tattalin arziki.

Mista Gomes ya kara da cewa kasar Guinea-Bissau, wadda akasarin kayayyakin da take fitarwa na albarkatun gona ne, irinsu gyadar yazawa ko “cashew nuts”, na iya amfani da wannan zarafi wajen fadada, da ingiza sarrafa kayayyaki a cikin gida.

A mataki na shiyya kuwa, Gomes ya yi kira da a karfafa, da tsara salon tattaunawa a hukumance, tsakanin kasashe membobin kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ko ECOWAS da bangaren Sin, ta yadda hakan zai taimaka wajen daidaita mizanin ingancin hajoji da bunkasa cinikayya. (Saminu Alhassan, Abdulrazaq Yahuz Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *