El-Rufai ya shafe kwanaki 30 a tsare ba a gurfanar da shi ba
[ad_1]
Wata guda bayan da Hukumar yaƙi da cin da hanci da rashawa ta ICPC ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, har yanzu ba a gurfanar da shi a gaban kowace kotu ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Wata guda bayan daHukumar yaƙi da cin da hanci da rashawa ta ICPC ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, har yanzu ba a gurfanar da shi a gaban kowace kotu ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Tun da farko, El-Rufai ya shafe dare biyu a hannun Hukumar EFCC kan zargin almundahanar kuɗi lokacin yana gwamna, kafin jami’an tsaro na farin kaya (DSS) su tafi da shi, sannan daga baya aka miƙa shi ga Hukumar ICPC.
A ranar 16 ga Fabrairu, tsohon Gwamnan ya amsa gayyatar da EFCC ta yi masa, inda jami’an bincike suka tuhume shi. Wannan ya biyo bayan gazawar jami’an tsaro wajen kama shi a filin jirgin saman Abuja lokacin da ya dawo daga ƙasar Masar.
Abin da ya faru a kotu
Lauyoyi sun bayyana cewa, kodayake kotu tana da ikon tsawaita lokacin tsare mutum, yin hakan ba tare da umarnin kotu ba ya saɓa wa doka a sashen 293 zuwa 296 na Dokar Shari’ar Manyan Laifuka (ACJA).
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa, ICPC ta samu umarnin tsare shi na kwanaki 14 daga wata Kotun Majistare da ke Bwari, Abuja, a ranar 19 ga Fabrairu, wanda aka sake sabuntawa.
Sai dai lauyoyin El-Rufai sun shigar da buƙatar ƙalubalantar tsawaita tsare shi, inda suka bayyana hujjoji da dama waɗanda aka sanya jiya a matsayin ranar yanke hukunci kansu.
Ana sa ran Alƙalin Majistare, Okechukwu Akweke zai yanke hukunci a ranar 19 ga Maris.
A cikin buƙatar da aka shigar, El-Rufai ya yi zargin cewa jami’an ICPC sun buƙaci ya janye daga harkokin siyasa a matsayin sharaɗin sakin sa, inda ya bayyana hakan a matsayin take haƙƙinsa na kundin tsarin mulki.
A cewar takardun ƙarar, ya fara kai kansa ga EFCC ne a ranar 16 ga Fabrairu inda aka ba shi beli, amma daga baya DSS ta kama shi ta miƙa shi ga ICPC ba tare da wata ƙwaƙƙwarar hujja ta shari’a ba, wanda hakan ya kai ga tsare shi ba bisa ƙa’ida ba.
Karar ta zargi manyan jami’ai, ciki har da shugaban ICPC da Darakta Janar na DSS, da tsare shi ba tare da haƙƙi ba. Lauyoyinsa sun kuma kafa hujjar cewa, umarnin tsare shi ba shi da inganci kuma lokacin tsare shi ya wuce kima ba tare da wata hujja ba.
Duk da haka, El-Rufai ya yi iƙirarin cewa an hana shi sadarwa da kowa, ciki har da iyalansa, lauyoyinsa, da kuma samun kulawar likita.
Kararrakin da ake yi ne suka dakatar da mu – ICPC
Da yake magana da ɗaya daga cikin wakilanmu a daren jiya, wani babban jami’i a ICPC ya bayyana cewa ƙararrakin da aka shigar a kan hukumar ne suka jinkirta gurfanar da shi. Ya ce dole ne a janye dukkan umarnin kotu da ke adawa da ICPC kafin hukumar ta iya gurfanar da tsohon gwamnan.
“El-Rufai ne da kansa yake jinkirta gurfanar da shi. Ya shigar da ƙara daban-daban a kan hukumar. Saboda haka, wasu daga cikin waɗannan ƙararrakin ya kamata a janye su kafin mu ci gaba bin matakan shari’a,” in ji jami’in.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link