Jama’ar gari sun kashe ’yan bindiga 3 a Sakkwato
[ad_1]
Wasu mazauna da ke aikin sa-kai a ƙauyen Bargaja da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, sun kashe wasu ’yan bindiga uku a wani artabu da ya faru a ranar Lahadi.
Rahotanni daga yankin sun ce ’yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare, inda suka kurɗo ta wasu hanyoyi da ke wajen gari domin yi wa al’ummar shigar ba-zata.
Wani jagoran al’umma a ƙauyen wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun ɓuya a kan bishiyoyi da ke kusa da maƙabartar ƙauyen, yayin da wasu suka shiga wani gida a wajen gari, inda suka yi karo da ’yan sa-kai da ke sintiri a yankin.
A cewarsa, ’yan bindigar sun kashe wani ɗan sa-kai guda ɗaya, lamarin da ya fusata kafin sauran ’yan sa-kan mayar da martani suka kashe uku daga cikin maharan a yayin musayar wuta.
Ya ƙara da cewa daga bisani maharan sun kashe wani ɗan sa-kai da ya ɓuya a cikin wani gida.
“Sun kashe ’yan sa-kai biyu, Umar Ibrahim da Abubakar Abdullahi na Mumini. Mu kuma mun kashe ’yan bindiga uku a yayin artabun,” in ji shi.
Wasu mazauna yankin sun ce maharan sun zo ne a ƙafa cikin sanɗa, bayan sun ajiye baburansu a wajen gari, sannan bayan artabun sun yi amfani da jaki wajen ɗaukar gawarwakin ’yan uwansu da aka kashe kafin su tsere.
Aminiya ta ruwaito cewa wannan lamarin dai ya jefa mazauna ƙauyen cikin fargabar dawowar ’yan bindigar domin ɗaukan fansa, inda wasu suka yi yunƙurin barin garin, sai dai shugabannin al’umma da kwamitin tsaron ƙauyen sun shawo kansu da su zauna.
Mazauna sun koka kan yawaitar hare-haren ’yan bindiga a yankin, da suka yi zargin cewa Bargaja na daga cikin ƙauyukan da ba su da jami’an tsaro duk da irin barazanar da suke fuskanta.
Sun yi kira ga gwamnatocin jiha da tarayya da su tura jami’an tsaro zuwa ƙauyen domin daƙile hare-haren da ke aukuwa akai-akai.
Da aka tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Sakkwato, Ahmad Rufai, ya ce rundunar na da masaniya kan harin da kuma asarar rayukan da aka yi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link