Tsohon ministan sufuri ya sauya sheƙa daga PDP zuwa ADC a Sakkwato
[ad_1]
Tsohon Ministan Sufuri, Alhaji Yusuf Suleiman, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP tare da komawa ADC.
Ya bayyana hakan ne cikin wata takarda da ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na mazaɓarsa ta Isa ta Arewa a Ƙaramar Hukumar Isa, a Jihar Sakkwato.
Alhaji Yusuf Suleiman, ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Matasa da Wasanni a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.
Ya ce ya ɗauki wannan mataki ne saboda rikicin shugabanci da ya addabi jam’iyyar PDP.
Ya ce: “Na yanke shawarar barin PDP ne saboda rikice-rikicen shugabanci da jam’iyyar ke fama da su, waɗanda har yanzu ba a samu mafita a kansu ba.”
Ya ƙara da cewa bayan shekaru da dama yana cikin jam’iyyar kuma yana bayar da gudunmawa ga ci gabanta, ya ga cewa lokaci ya yi da zai fice.
Suleiman, ya ce ya koma jam’iyyar ADC ne domin ya ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ci gaban ƙasa da kuma taimakawa wajen magance matsalolin rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziƙi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link