Tsagin Wike ya gudanar da taron zaɓen shugabannin PDP a Kano
[ad_1]
Tsagin Nyesom Wike na jam’iyyar PDP, ya gudanar da taron zaɓen shugabannin jam’iyyar na Jihar Kano a ranar Asabar, inda aka fitar da sabbin shugabanni ta hanyar yin maslaha.
Taron ya gudana ne kwanaki kaɗan bayan wani hukunci da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na soke shugabannin jam’iyyar a matakin jiha waɗanda Tanimu Turaki ke jagoranta.
Jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ne, suka sa ido kan yadda aka gudanar da taron.
A yayin taron, an zaɓi Bello Gambo Bichi a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na jihar.
Sauran waɗanda aka zaɓa sun haɗa da Ali Mati Shantake a matsayin Sakataren Kuɗi, Hafsat Abubakar a matsayin Shugabar Mata, Musa Baba Dala a matsayin Sakataren Yaɗa Labarai, da kuma Auwal Ya’u a matsayin Shugaban Matasa.
Haka kuma, an zaɓi Abdullahi Umar a matsayin Mai Ba da Shawara kan Harkokin Shari’a, yayin da Lawan Shehu Yakasai ya zama Ma’aji.
Shugaban kwamitin zaɓen da jam’iyyar ta tura jihar, Aminu Abdullahi Taura, ya bayyana cewa an gudanar da taron ne bayan an rushe shugabannin jam’iyyar a matakin mazaɓu da ƙananan hukumomi a faɗin jihar.
Ya ƙara da cewa taron wani ɓangare ne na gyaran fuska da ake yi wa jam’iyyar, yana mai iƙirarin cewa ’yan Najeriya da dama sun gaji da mulkin jam’iyyar APC, kuma suna muradin PDP ta dawo kan mulki.
Taura, ya bayyana cewa an zaɓi mambobi 29 na kwamitin gudanarwa na jihar ne ta hanyar yarjejeniya tsakanin masu ruwa da tsaki da kuma kwamitin riƙo.
Ya jaddada cewa PDP jam’iyya ce guda ɗaya duk da saɓanin da aka samu a baya, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin sulhu domin haɗa kan dukkanin shugabanninta.
Shugaban Matasa na PDP na ƙasa, Ibrahim Bala Aboki, wanda shi ma ya yi jawabi a wajen taron, ya bayyana cewa ba a taɓa samun matashi a irin wannan matsayi na ƙasa ba a tarihin jam’iyyar sai a zamanin Nyesom Wike.
Ya kuma yi watsi da zargin cewa jam’iyyar ta rabu gida biyu, yana mai tabbatar da cewa an gudanar da tarukan zaɓen cikin nasara a mazaɓu 448 da ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.
A ƙarshe, taron ya amince da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a zaɓen 2023, Muhammad Sani Abacha, a matsayin jagoran jam’iyyar a Jihar Kano, sakamakon gudunmawar da yake bayarwa ga ci gaban jam’iyyar.
Shugabannin sun bai wa mambobinsu tabbacin cewa za a ci gaba da sulhu domin ƙarfafa jam’iyyar gabanin zaɓuka masu zuwa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link