Amurka ta umarci wasu jami’an diflomasiyyarta su fice daga Oman
[ad_1]
Amurka ta umarci wasu ma’aikatan diflomasiyyarta waɗanda ayyukansa ke da rangwamen muhimmanci da su gaggauta ficewa da ƙasar Oman, yayin da yaƙi ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da hakan a cikin wata sabuwar sanarwar gargaɗi ga ’yan ƙasarta, inda ta ce akwai barazanar tsaro sakamakon hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da ake zargin na Iran ne.
Sanarwar ta kuma gargaɗi Amurkawa da su yi taka-tsantsan saboda yiwuwar ci gaba da hare-hare da kuma tangarɗar zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci a yankin.
Rahotannin kafafen yaɗa labarai na Oman sun ce a ranar Juma’a wasu jiragen marasa matuƙa sun kashe mutum biyu a arewacin ƙasar.
Harin na zuwa ne yayin da Iran ke ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya a wasu ƙasashen makwabta, lamarin da ya ƙara tayar da hankali game da tsaro a yankin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link