Gwamnatin Kano Ta Amince Da Ayyuka Na Sama Da Biliyan ₦310

[ad_1]

Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da aiwatar da ayyuka dan darajarsu ta haura Naira biliyan 310 domin inganta ababen more rayuwa a fannin ilimi, da lafiya, da gidaje da sauran muhimman fannoni a faɗin jihar.

An yanke wannan hukunci ne a zama na 38 na majalisar da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya jagoranta a zauren majalisar da ke Fadar Gwamnatin Kano. Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar bayan kammala taron.

  • Kotun Ƙoli Za Ta Yanke Hukunci Kan Rikicin Masarautar Kano
  • Lauyoyin Gwamnatin Kano Sun Tsunduma Yajin Aiki, Sun Rufe Ma’aikatar Shari’a

A cewarsa, majalisar ta amince da ayyuka da ƙudurori da kudinsu ya kai N310,266,203,046 a fannoni daban-daban na tattalin arziƙin jihar. A ɓangaren ilimi kuwa, an amince da kashe Naira miliyan 238.02 domin biyan kuɗin JAMB ga ɗaliban da suka cancanta a fadin jihar, tare da gyaran makarantu a ƙananan hukumomi da dama.

Haka kuma an amince da ayyukan hanyoyi da gine-gine da suka haɗa da gyaran shalƙwatar hukumar kashe gobara ta jihar, ƙarin wasu ayyuka a Asibitin Yara na Hasiya, da kula da titin Rimin Auzinawa a ƙaramar hukumar Ungogo da kuma gina hanyoyin Ladanai. Majalisar ta kuma amince da Naira biliyan 13.2 domin aiwatar da ayyukan mazabu na shekarar 2026 a faɗin jihar.

A ɓangaren gidaje, majalisar ta amince da sama da Naira biliyan 113 domin gina gidaje 480 a wani babban shirin gidaje mai suna Gida Gida Mega City a Rijiyar Gwan-Gwan. Haka kuma an amince da sayen injinan wankin ƙoda ga cibiyar Abubakar Imam Urology Centre da kuma kayan aikin haƙora ga asibitocin jihar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *