Za a Gudanar Da Tattaunawa Kan Batun Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka a Faransa Daga Ranar 14 Zuwa 17 Ga Watan Maris

[ad_1]

Ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, bisa yarjejeniya tsakanin bangarorin Sin da Amurka, za a gudanar da tattaunawar kasuwanci tsakanin bangarorin biyu a karo na 6, a Faransa daga ranar 14 zuwa 17 ga watan Maris.

Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, zai jagoranci tawagar Sin don halartar taron. Bangarorin biyu za su tattauna kan batutuwan kasuwanci da suka shafe su bisa matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a taron koli na Busan da sauran tattaunawar da suka yi ta wayar tarho.(Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *