Gusau ya zama sabon shugaban sabuwar tashar jirgin saman Zamfara
[ad_1]
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya naɗa Kabiru Yahaya a matsayin sabon shugaban sabuwar tashar jirgin saman jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne, ya bayyana hakan.
Ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da sabuwar tashar jirgin saman ta fara aiki cikin ƙanƙanin lokaci.
A cikin wata sanarwa da Babban Mashawarcin Gwamnan kan Yaɗa Labarai, Suleiman Ahmad Tudu, ya fitar, ya ce samar da tashar jirgin saman zai taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci na ƙasa da ƙasa.
Hakazalika, ya ce tashar za ta jawo masu zuba jari, da kuma ƙarfafa tattalin arziƙin Jihar Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya.
Ya ce: “Kabiru Yahaya ƙwararre ne a fannin harkokin jirgin sama, wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana aiki a wannan fanni da kuma gudanar da shi.”
Sanarwar ta ƙara da cewa Yahaya ya taɓa riƙe muƙamin manaja a Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA), sannan ya taɓa zama mataimaki na musamman ga babban daraktan hukumar a matakin ƙasa.
Tudu ya ƙara da cewa: “Ya yi karatun difloma da kuma digiri na biyu a fannin Tsara Zirga-zirgar Jiragen Sama a Jami’ar Legas (LASU).
“Sannan ya samu takardar shaidar kammala horo kan sadarwar jiragen sama a Kwalejin Horas da Fasahar Jirgin Sama da ke Zariya (NCAT).”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link