Muna son kawar da barazanar da Iran ta daɗe tana yi mana — Isra’ila
[ad_1]
Gwamnatin Isra’ila ta ce ba ta da niyyar dawwama tana yaƙi da Iran, tana mai jaddada cewa idan lokaci ya yi za su ajiye makamai.
Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Gideon Saar ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a Jerusalem.
Saar ya jaddada cewa Isra’ila za ta ci gaba da yaƙin har sai lokacin da ita da abokan hulɗarta suka ga ya dace a dakatar da shi.
Ya kuma ce Isra’ila za ta tattauna da babbar ƙawarta, Amurka, domin tantance lokacin da ya dace a kawo ƙarshen rikicin.
A cewarsa, Isra’ila ba ta muradin ta ci gaba da yaƙi mara iyaka ba, amma tana son kawar da barazanar da Iran ke yi mata a tsawon lokaci.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link