Iran ta kama wani ɗan ƙasar waje kan zargin leƙen asiri
[ad_1]
Ma’aikatar tattara bayanan sirri ta Iran ta sanar da kama mutane 30 da ake zargi da aikata leƙen asiri, ciki har da wani baƙo ɗan ƙasar waje, a rana ta 11 da fara yaƙin Gabas ta Tsakiya.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Mizan Online na ma’aikatar shari’a, hukumomin Iran sun ce an kama baƙon mutumin ne a arewa maso gabashin ƙasar.
Sanarwar ta ce ana zargin mutumin da yi wa wasu ƙasashe biyu na yankin Tekun Fasha leƙen asiri ne a madadin abin da ta kira “maƙiya Amurka da Yahudawa.”
Hukumomin sun ce ana zarginsa da aika bayanai ga abokan gaba kan wurare da ayyukan jami’an ’yan sanda da sojoji, da kuma wasu muhimman cibiyoyin soji.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana ƙasar da mutumin ya fito ba, kuma ba ta fayyace ranar da aka kama shi ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link