Ramadan: ‘Yansanda Sun Buƙaci A Sanya Ido A Kano A Goman Ƙarshe
Rundunar ‘Yansandan Nijeriya da ke hedikwatar Shiyya ta Ɗaya a Jihar Kano, ta buƙaci mazauna jihar, musamman Musulmi, su kasance cikin shiri da sanya ido a kwanakin goman karshe na watan Ramadan.
A cikin wata sanarwar tsaro da aka fitar ranar Litinin, kakakin rundunar a shiyyar, DSP Abdullahi Hussaini, ya ce wannan gargaɗi ya fito ne daga Mataimakin Sufeto Janar na ‘yansanda mai kula da shiyyar, Garba Ahmed.
- SAHUR (Falalarsa Da Fa’idojinsa) Na 21
- Majalisar Dattawa Za Ta Gayyaci Kyari Kan Zargin Giɓin Kuɗi Har Naira Tiriliyan 210 A NNPCL
Ya tunatar da masu ibada da su kasance masu lura da tsaro, domin a wannan lokaci mutane da dama kan halarci salla cikin dare.
Rundunar ‘yansandan ta ce wasu ɓata-gari na iya amfani da wannan lokaci wajen aikata laifuka.
Saboda haka, an shawarci masu ibada su guji bin hanyoyin da babu mutane, su kula da kayayyakinsu, sannan su riƙa kai rahoton duk wani abun zargi ga ofishin ‘yansanda mafi kusa.
Rundunar ta kuma tabbatar wa da jama’a cewa tana ci gaba da ɗaukar matakai domin kare rayuka da dukiyoyinsu.
A gefe guda ta buƙaci al’umma su ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.