Sin Za Ta Ci Gaba Da Samar Da Sababbin Damammaki Ga Kasashe Masu Tasowa Ta Hanyar Ci Gabanta Mai Inganci

[ad_1]

An gudanar da taron karawa juna sani kan ci gaba mai dorewa da hakkin tattalin arziki, zamantakewa da al’adu a taron kasa da kasa na kwamiti mai kula da hakkin dan Adam karo na 61 na MDD a ranar 5 ga watan nan. Mataimakiyar shugaban tawagar Sin a taron kasa da kasa na kwmamiti mai kula da hakkin dan Adam karo na 61 na MDD Li Xiaomei, ta halarci taron kuma ta bayyana ra’ayi da matsayar kasar Sin.

Li Xiaomei ta nuna cewa, shawarar ci gaban duniya da Sin ta gabatar ta sanya samar da kudaden ci gaba a matsayin muhimmin fagen hadin gwiwa, kuma shawarar ta riga ta tattara sama da dala biliyan 23, don tallafawa ci gaba da bunkasar kasashe masu tasowa.

Kazalika, Sin ta gabatar da kudurori kan hakkin tattalin arziki, da zamantakewa da al’adu, da kuma hakkin ci gaba don inganta hakkin dan Adam a kwamitin, matakin da ya ingiza karfin hadin gwiwar da zai amfani mabambantan bangarori. Har ila yau, Sin ta raba ra’ayoyi da ci gaban da ta samu na kare hakkin dan Adam, da kuma gina sababbin dandaloli don horar da kwararrun ma’aikata, da gina makamar aiki a kasashe masu tasowa.

Li Xiaomei ta kara da cewa, bangaren Sin yana fatan samar da sababbin damammaki ga kasashe masu tasowa ta hanyar ci gabanta mai inganci, ta yadda za ta inganta hakkin ci gaba, da hakkin tattalin arziki, da kuma zamantakewa da al’adu da sauran hakkokin bil’adama, ba tare da barin kowa a baya ba. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *