Sin Za Ta Inganta Sufuri Mai Amfani Da Fasahohin Zamani Da Makamashi Mai Tsafta

[ad_1]

Ministan sufuri Liu Wei ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin za ta sa kaimi ga inganta sashen sufuri mai amfani da fasahohin zamani da sauyawa zuwa makamashi mara gurbata muhalli a cikin shirin shekaru biyar-biyar karo na 15 da za a aiwatar tsakanin 2026 zuwa 2030.

Liu ya fada a gefen taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin cewa, a cikin shekaru 5 masu zuwa, kasar za ta sa kaimi ga yin amfani da fasahar kirkirarriyar basira a sashen sufuri, da yin kokari wajen habaka amfani da fasahohin zamani a manyan hanyoyin mota, da tashoshin jiragen ruwa, da fiton kayayyaki.

Har ila yau, kasar za ta kuma karfafa bunkasa yankuna da tashohin sufuri masu karancin fitar da hayaki mai gurbata muhalli, a wani bangare na kokarin habaka ci gaban sufuri mai karancin fitar da hayaki mai gurbata muhalli, kana Liu ya kara da cewa, kasar Sin za ta kara yin amfani da kayayyakin sufuri masu amfani da makamashi mai tsafta kamar motocin sabbin makamashi da jiragen ruwa a tsakanin wannan lokacin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *