Kamfanonin Kasa Da Kasa Sun Nuna Gamsuwa Da Dimbin Damarmakin Da Kasuwar Kasar Sin Ta Samar
[ad_1]
A yayin taron NPC da na CPPCC, muhimman tsare-tsare da sabbin kalmomi a cikin rahoton aikin gwamnati, sun zama muhimmiyar taga ga kamfanonin kasashen waje ta kallon kasar Sin, tare da tsara shirinsu a nan kasar Sin.
Babban jami’in kamfanin Yihai Kerry Arawana Holdings Co. Ltd Tu Changming ya bayyana cewa, rahoton aikin gwamnatin ya gabatar da bukatar gina babbar kasuwar Sin mai karfi a cikin gidanta, da kara nauyin aljihun jama’a, tare da bunkasa tattalin arziki. Wannan yana nufin cewa, kasuwar cin abinci, da ta man girki za ta ci gaba da girma, kuma bukatun jama’a za su canza daga cika ciki zuwa cin abinci mai kyau da lafiya. Wannan ya yi daidai da tsarin dukkannin sassan kamfanonin.
Shi kuwa shugaban kamfanin Sanofi na babban yankin Sin Shi Wang, cewa ya yi saurin kashe kudaden bincike a Sin ya yi matukar karuwa, inda yawan kudaden da ake kashewa a wannan bangare ya karu sosai. Ya ce fiye da kashi 90% na muhimman kayayyakin da kamfanin ke samarwa a duniya, kasuwar Sin da sauran kasuwannin duniya suna gwada su da yin bincike kan su tare da kamfanin. Kazalika, jami’in ya yi fatan kamfanin zai shiga aikin kirkire-kirkiren kwayoyin halitta, da magunguna da Sin ke gudanarwa, da kuma amfani da wadannan sababbin kayayyaki domin hidimtawa marasa lafiya a duniya. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link