Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 23 a Nairobi
[ad_1]
Mahukunta a jiya Asabar sun tabbatar da cewa aƙalla mutum 23 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a Nairobi, babban birnin Kenya.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa ruwan sama mai ƙarfi da ya sauka daren Juma’a ya mayar da manyan titunan birnin tamkar koguna, inda ya mamaye dubban gidaje da shaguna.
Jami’an ceto na ci gaba da laluben gawarwaki da kuma mutanen da suka maƙale, yayin da lalacewar ababen more rayuwa ta bazu a tsakanin unguwannin marasa galihu zuwa yankunan mawadata kamar Parklands.
Wasu mazauna yankin sun ce ruwan da ya ɓallo daga ya kwashe motoci tare da mamaye shaguna, abin da ya janyo asarar dukiya mai yawa.
Hukumar Ba da Agaji ta Kenyan Red Cross Society ta ce ambaliyar ta jawo ɓarna a sassa da dama na birnin da kuma wasu ƙananan hukumomi na ƙasar.
Shugaban Kenya, William Ruto, ya ce ya bayar da umarnin tura tawagar gaggawa domin taimaka wa ayyukan ceto.
Sai dai wasu ’yan ƙasar sun nuna fushi ga gwamnan Nairobi, Johnson Sakaja, kan zargin rashin samar da ingantaccen tsarin magudanan ruwa da zai rage irin wannan ambaliya.
Masana sun ce yankin gabashin Afirka na fuskantar sauye-sauyen yanayi a cikin shekaru 20 da suka gabata, wanda ke janyo tsananin ruwan sama ko fari a wasu lokuta.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link