Matsalar tsaro ba ta ƙara ta’azzara ba a Najeriya — Bwala
[ad_1]
Daniel Bwala, Mai Bai Wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shawara kan harkokin sadarwa, ya ce matsalar rashin tsaro a Najeriya ba ta ƙara tsananta ba duk da hare-haren da ake samu a wasu sassan ƙasar.
A ’yan kwanakin nan Najeriya ta fuskanci wasu hare-hare da suka haɗa da sace mutane da kuma kai wa wasu yankuna hare-hare.
A farkon wannan mako, ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP sun sace mata da yara sama da 100 a ƙauyen Ngoshe da ke Jihar Borno.
Da yake magana yayin wata tattaunawa a tashar Al-Jazeera a shirin Head to Head da aka yi a birnin Landan, Bwala ya ce Gwamnatin Najeriya na ƙoƙarin magance matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.
“Na yarda cewa akwai matsalar rashin tsaro a Najeriya, amma cikin shekaru biyu na wannan gwamnati an samu zaman lafiya sosai. Babu wata ƙasa a duniya da ba ta da matsalar tsaro gaba ɗaya,” in ji shi.
Ya kuma ce Najeriya na haɗin gwiwa da wasu ƙasashe domin yaƙi da ta’addanci da inganta tsaro a faɗin ƙasar.
“Ba za mu ce matsalar rashin tsaro na ƙara tsananta ba. A matsayinmu na gwamnati, muna aiki dare da rana domin magance wannan matsalar,” in ji shi.
Bwala ya kuma zargi wasu kafafen yaɗa labarai na ƙasashen yamma da yi wa Najeriya da Afirka baƙin fenti.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta ɗauki matakai da dama wajen yaƙi da ta’addanci, ciki har da kama wasu shugabannin ’yan ta’adda da kuma yin aiki tare da ƙasashen waje domin ƙarfafa tsaro.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link