Majalisar Dattawa ta gayyaci Mele Kyari kan rashin bayanin N210trn a NNPCL
Kwamitin Kula da Asusun Gwamnati na Majalisar Dattawa, ya gayyaci tsohon shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, domin ya yi bayani kan wasu kuɗaɗe da yawansu ya kai Naira tiriliyan 210 da ake zargin ba a bayyana yadda aka kashe su ba.
Kwamitin ya ce kuɗaɗen sun shafi shekarun 2017 zuwa 2023, lokacin da Kyari yake jagorantar kamfanin.
Baya ga Kyari, kwamitin ya kuma gayyaci tsohon babban jami’in kula da kuɗi na kamfanin, Umar Ajia Isa.
Hakazalika, ya gayyaci tsohon babban manajan zuba jari, Bala Wunti, domin ya yi bayani.
Shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada, ne, ya bayar da umarnin gayyatar a ranar Alhamis bayan da kwamitin ya duba rahotannin binciken kuɗi da suka shafi kamfanin.
Kwamitin, ya kuma yi gargaɗin cewa zai iya fitar da sammacin kama duk wanda aka gayyata idan bai bayyana a gaban kwamitin ba a ranar da za a sanar nan gaba.
Sanata Wadada ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan kammala taron kwamitin.
Ya ce ana sa ran tsoffin shugabannin kamfanin za su bayyana tare da shugabannin kamfanin na yanzu, ƙarƙashin jagorancin sabon Babban Darakta, Bayo Ojulari, da kuma masu binciken kuɗi na waje da suka yi aiki da kamfanin a lokacin da ake magana a kai.