Kotu Ta Bayar Da Malami Da Iyalansa Beli Kan Naira Miliyan 200 Kowannensu

[ad_1]

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba tsohon Ministan Shari’a na Tarayya, Abubakar Malami, da matarsa Asabe Bashir da kuma ɗansa Abdulaziz Malami beli a shari’ar zargin sama da faɗi da kuɗi da ake yi musu.

Alkalin kotun, Joyce Abdulmalik, ta bayar da belin na Naira miliyan 200 ga kowannensu tare da sharaɗin samun mutane biyu da za su tsaya musu a matsayin masu lamuni da adadin kuɗin iri ɗaya.

  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Malami Da Matarsa A Benue
  • Mutum 1 Ya Rasu Yayin Da Sojoji Suka Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Ƙauyukan Benue

Kotun ta kuma umurci ɗaya daga cikin masu lamunin ya ajiye takardar mallakar gida a yankunan Maitama ko Asokoro, tare da umartar waɗanda ake tuhuma su mika fasfo ɗinsu na ƙasashen waje ga kotu.

Alƙalin ta ce har sai sun cika duk sharudan belin, Malami da matarsa da ɗansa za su ci gaba da zama a hannun hukumar grantvt#₦, sannan ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga Maris, 2026 domin fara shari’a.

Ana zargin Malami tare da iyalansa da sama da a kimanin Naira biliyan 8.7 ta hanyar kamfanoni da sayen kadarori masu daraja a Abuja da kuma jihohin Kano State da Kebbi State, yayin da ake kuma tuhumar sa da wasu laifuka da suka haɗa da zargin tallafa wa ta’addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ƙaa’ida ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *