Ban Fuskanci Matsala Ba A Gwagwarmayar Shiga Harkar Fim —Asiya Muhammad

[ad_1]

Kamar kowane mako shafin RUMBUN NISHAƊI, shafi ne da ya saba zaƙulo muku fitattun jarumai manya da ƙananan, daga cikin masana’anatr shirya finafinan hausa ta Kannywood.

Yau ma shafin na tafe da wata fitacciyar jarumar wato, HAJIYA ASIYA MUHAMMAD wacce aka fi sani da UWAR DASHI. Inda ta fayyacewa masu karatu zare da abawa na wasu abubuwan dake faruwa a cikin masana’antar Kannywood, kana fitacciyar jarumar ta yi wani kira ga masu yunƙurin shiga cikin masana’antar ta Kannywood, har ma da wasu batutuwan masu yawa da suka shafi rayuwarta da kuma sana’ar ta.

  • Kotu Ta Yanke Wa Jarumar Kannywood Samha Hukuncin Ɗaurin Wata 6 A Gidan Yari
  • Na Shekara Biyu Ina Kokarin Shawo Kan Mahaifina Ya Amince Da Shigata Kannywood —Iklima Umar Argungun

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar Jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA kamar haka;

Da farko za ki faɗawa masu karatu cikakken sunanki.

Sunana Hajiya Asiya Muhammad, amma an fi sanina da Anti Asiya uwar dashi. Uwar dashi ya samo asali ne sanadiyyar kamfanina me suna ‘Uwar Dashi Film Production’, kuma na yi wani fim me suna Uwar dashi, nayi ta cakwakiyar rigimar dashi a ciki, shi ne ake ce min Uwar’dashi.

Ko za ki faɗawa masu karatu ɗan taƙaitaccen tarihinki?

An haife ni a Kaduna ‘Jama’a Road by Lagosstreet’. Amma asalin mahaifina Bakatsine ne, haifaffen Huntuwa. Mahaifiyata kuma Bagobura ce, da idan Malami ya je gari da almajirai to, sai ya sauka a gidan maigari, maigari sai ya datsa masa fili ya ce “to, je ka gina”, idan ka gina ya zama naka. Babbanmu da ya zo Kaduna aka bashi wannan guri, shi ne sai ya gina. Sai da ya gama gini gabaɗaya ya je ya ɗauko mahaifiyarmu tare da kishiyarta.

Wane rawa kike takawa a cikin masana’antar Kannywood?

Ina taka rawa matsayin jaruma, kuma me shiryawa.

Me ya ja hankalinki har kika tsunduma cikin masana’antar Kannywood?

Abin da ya ja hankali na shi ne, zan ga mutum ya mutu sama da shekara goma, biyar, takwas, ashirin, amma an nuno shi a fim mutane su yi ta yi masa addu’a. A duk lokacin da za a nuno matacce sai an yi masa addu’a, sanan idan mutum ya mutu kuma kan kace kwabo labarin duk yayi tambari wane ya mutu. To, shi Allah azizul’gafuru ne, idan ya ga dama sai yaƙi karɓar addu’ar jininka, amma wani can bare baka taɓa ganinsa ba, shi ma bai taɓa ganinka ba sai a ‘Teleɓision’ ko a waya, sai ka ga ubangiji ya karɓi addu’ar sa. Wannan ne ya ja hankali na saboda ko da na mutum na sanu masu yi min addu’a.

Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?

Ban wani daɗe sosai ba, ba na tunanin na shekara shida a Kannywood.

Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance?

Ba wata gwagwarmaya wallahi da na sha, saboda ta hanya me sauƙi na shige ta.

Ya batun iyaye ko ƴan’uwa lokacin da za ki sanar musu kina sha’awar fara fim, shin kin samu wani ƙalubale daga gare su ko kuwa?

Lokacin da na shiga mahaifiyata ce take da rai, kuma ita mace ce me sauƙin kai babu ruwanta. Dan lokacin da aka kira ni bayan na dawo na sauka a ɗakinta. Gidanmu daban-daban ne, ita tana ɗaya sabon gidana ne, ni kuma ina wani gidan daban. Na sanar mata da komai, ta ce duk abin da ka mayar da shi sana’a, shi ma zai mayar da kai sana’a. Saboda haka idan kin ɗauka wannan abun sana’a ne ubangiji Allah ya baki sa’a. Har ta kai ta kaho idan za ni har ƙofar gida take rako ni. Yarana ne ma suka nuna ba sa son abun, ɗana ɗaya a duniya sai ƙanina tun yana shekara uku na riƙe shi. Suka nuna kyamatar abun na zauna na fahimtar da su, sai ta kai ta kawo ma har idan nayi latti zan kira ɗaya daga cikinsu na ce ya zo ya kai ni.

Da wane fim ki ka fara kuma ya farkon farawar ya kasance?

Na fara da kwana casa’in. Watarana da dare ina bacci wajen tara, sai wani Auwalu Jauro ya kira ni wanda yake fitowa ‘Assistant commissioner’ a kwana casa’in. Lokacin kwana na shida da dawowa daga Saudia, ya ce na zo dan Allah ga wani abu, na ce “mene ne?” ya ce ni dai na zo. Yayi min kwataccen inda yake, ya ce min wani waje ne zan ɗan riƙe musu. ‘Scene’ ɗaya ne rak! nayi a kwana casa’in ɗin, kuma a ranar aka fara ɗora min ‘camera’.

Kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?

Taɓ! Ko daga bara zuwa bana wallahi in kashe ni za a yi ban sani ba, kuma ina yin bidiyo-bidiyo irin na ‘comedy’ ɗin nan, na kan fito musu a Uwa. Dan ni a halin yanzu da a kira ni fim ma gara a kira ni wannan ɗan ‘comedy’ ɗin, dan yafi alheri yafi samu. Saboda yaran suna kimanta ni, fiye da yadda ake zato. Sai na je fim na yi na tashi ga kuɗin mota na sha da sauran abubuwa amma a ɗauki N3000 a ba ni, tunda ko kwanan nan na yi haka to, amma abin da ya sa bai dame ni ba saboda fim ɗin babban fim ne. To, mu shi yake jan hankalinmu za a ce ai an ganka a babban fim. Amma wallahi sai a kira ni ‘comedy’ a ɗauki N10,000 a ba ni, N8000 a bani. Wannan ɗan ‘comedy’ da ake haskawa a Tiktok. Kuma ba wani ‘scene’ ne me yawa ba, gajeru ne, wani ma yaho kawai ake yi da ‘yar wayar. A awa ɗaya sai a yi waje takwas a gama.

Ko za ki iya faɗowa masu karatu sunayen wasu daga cikin finafinan da ki ka fito?

Akwai; Hagu da Dama, na Abba Ɗorayi. Takun Saƙa, na Abba Ɗorayi. Ƙalubale, Hauwa Kulu, na Maishadda. Bana Bakwai, na Maishadda. Wutar Kara, na Maishadda. Wata Shida, na fito a matar Ali Nuhu, uwar Adam Zango, Laure na fito a babar Yawale. Sai finafinan kamfanina kusan guda biyar da suke gab da fitowa, akwai; Uwar Dashi, Uwar Dillaliya Dila, Wata Suruka, Nabil, Bada Yawuna Ba.

Cikin finafinan da ki ka fito, wane fim ne ya zamo bakandamiyyarki/wanda ki ka fi so?

Hagu da Dama fim ɗin Abba Ɗorayi, ina son fin ɗin nan. Wanda na fito a sunan Baba Ladi, wanda muka yi da KB International.

Ko akwai wani fim wanda ki ka yi da-kin-sanin fitowa cikinsa?

Eh, akwai. Fim ɗin wasu ƴan tagwaye, ni wallahi ban ma san sunan fim ɗin ba. Fim ɗin wasu ƴan biyu da suke zuwa daga Lagos ne ko Abuja ne. Daraktan ina jin kunyarsa ba zan iya faɗar sunansa ba. Na yi da-na-sanin shiga fim ɗin nan, saboda nayi asara sosai, ta kaya na, sarƙata, ɗan kunne na, zobe na, duk na tattara su Allah ya sa ba na gwal bane. Amma su ma za su kai kimanin N25,000. Na saka su a cikin aljihun riga ta, ta shadda. Da aka ce na ƙauye ne ba yi za a yi ba, na saka ta a rigata ta shadda na ƙudundune. Sai da na zo gida na nemi rigar nan na rasa, da awarwaro, sarƙa, zoben duk suna cikin rigar nan har rana me kamar ta yau sai dai gobe tashin alƙiyama. A ƙarshe na yi musu aiki kusan kwana huɗu aka ce za a ban N10,000, dakyar ta fito. Da ta fito ɗin ma suna baƙin ciki suna jin haushi da suka ba ni. Saboda faɗan da yaran yayi min ɗan cikina wallahi za ki mamaki “An ce za a cinye miki ne!, ko cewa akai za a cinye miki kuɗinki?”. Ko kuɗin mota ba bani suka yi ba, ba ma shi ya turon ba sai ya bawa Hussaininsa ya turo min. Ko da suka turo babu wanda ya kira ni ya ce ga kuɗin ki nan sai ni ina dube-dube na gani.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *