Martanin Da Sin Ta Mayar Kan Yunkurin Japan Ya Dace Da Muradun Duniya

[ad_1]

Kwanan nan, ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta sanar da sanya kamfanonin Japan 20 a cikin jerin sunayen wadanda aka hana sayar musu da kayayyakin kasar Sin da kuma wasu kamfanoni 20 da aka sanya su a cikin jerin wadanda ake sa ido a kansu. Wannan wani mataki ne na mayar da martani da ya dace bayan sanarwar karfafa kayyade fitar da kayayyakin ayyukan farar hula da na soji zuwa Japan fiye da wata 1 da ya gabata, da nufin dakile yunkurin Japan na “farfado da karfin soja” da kuma burin mallakar makamin nukiliya, da kuma kare zaman lafiya a yanki da ma duniya. Manazarta na ganin cewa, matakin Sin na da adalci, kuma bisa gaskiya, sannan ya dace da doka da muradun duniya baki daya, kuma ya bayyana yadda kasa mai girma ta sauke nauyin dake wuyanta.

Wajibi ne a aiwatar da takunkumi a kan wadannan kamfanonin samar da kayan aiki na Japan, duba da ainihin ayyukan da suke gudanarwa. Kamfanoni irin su Mitsubishi Heavy Industries da Kawasaki Heavy Industries da aka sanya a cikin jerin sunayen wadanda aka hana fitar musu da kayan Sin, ana iya kiransu da “gadon yaki” na sojan Japan. Su ne manyan kamfanoni da suka kera makamai a lokacin yakin duniya na biyu, kuma a yanzu sun zama sahun gaba na “farfado da karfin soja” a Japan, kana ayyukansu sun riga sun kawo barazana ga tsaron yanki.

Zaman lafiya da ci gaba su ne burin dan Adam har abada, kuma su ne fatan gama-gari na kasashen gabashin Asiya. Karfafa hana fitar da kayayyaki na Sin zuwa Japan ba ramuwar gayya ta tattalin arziki ba ce, a’a, mataki ne mai karfi na mayar da martani ga matakai masu kawo hadari ta fuskar soja da Japan ta dauka dake kawo barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yanki, kuma hanya ce mai inganci ta dakile “farfado da karfin sojan Japan”.

Ya kamata gwamnatin Japan ta farka daga mafarkinta cewa, neman fadada ayyukan soja, da keta tsarin kasa da kasa da aka shimfida bayan yakin duniya na biyu, da farfado da ra’ayin amfani da karfin soja, za su sake jefa jama’arta cikin mawuyacin hali. Ya kamata al’ummomin kasa da kasa su hada karfi da karfe don hana farfado da karfin soja a Japan, da kare nasarorin da duniya ta samu a yakin duniya na biyu, da kuma kiyaye zaman lafiya da wadata a duniya tare. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *