Karfin Sin A Fannin Kere-kere Na Taimakawa Nahiyar Afrika Komawa Ga Amfani Da Makamashi Mai Tsafta
[ad_1]
Ministan kula da harkokin makamashi na kasar Madagascar, Ny Ando Ralitera, ya ce karfin kere-kere da kasar Sin take da shi a bangaren makamashi mai tsafta, ya taimaka wajen gaggauta komawar kasashen nahiyar Afrika ga amfani da makamshi mai tsafta.
Da yake hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Alhamis, a gefen taron kungiyar raya yankin kudancin Afrika (SADC) na Makon Makamashi mai Dorewa, a birnin Victoria Falls na Zimbabwe, Ralitera ya ce kayayyakin kasar Sin masu arha da matukar gogewar da kasar ke da ita a bangaren makamashi mai tsafta, sun samar wa nahiyar Afrika gagagrumin taimako.
A cewarsa, Madagascar na hada hannu sosai da Sin a bangaren samar da lantarki da makamashi. (FMM)
[ad_2]
Source link