‘Yan Majalisar Dokokin Adamawa 6 Sun Fice Daga Jami’yyar PDP
‘Yan majalisa shida na jam’iyyar PDP a Majalisar Dokokin Jihar Adamawa sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar.
Hakan ya sa adadin ‘yan PDP da suka fice daga jam’iyyar cikin kwanaki biyu ya kai bakwai, bayan wani ɗan majalisa da ya fara ficewa tun da farko.
- Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Matakan Kakaba Haraji
- Atiku Ya Nemi Gwamnati Ta Fayyace Dalilin Tsare El-Rufai
Daga cikin waɗanda suka fice akwai Mataimakin Kakakin Majalisar, Mohammed Buba Jidjiwa, tare da wasu ‘yan majalisa biyar daga mazaɓu daban-daban.
Ficewar tasu na zuwa ne a lokacin da ake ta raɗe-raɗin cewa gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri, na shirin komawa jam’iyyar APC.
Sai dai ‘yan majalisar ba su bayyana jam’iyyar da za su koma ba, amma ana hasashen cewa APC za su koma.