Atiku Ya Nemi Gwamnati Ta Fayyace Dalilin Tsare El-Rufai
[ad_1]
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya nuna matukar damuwa game da tsare tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yana mai kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bayyana wace hukumar tsaro ce ke tsare da shi kuma akan wane dalili.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata da rana, Atiku ya bayyana lamarin a matsayin “abin damuwa” kuma ya yi kira ga hukumomi da su fayyace lamarin a fili ba tare da wani nuƙu-nuƙu ba.
- Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 7
- Tinubu Ya Buƙaci Gwamnoni Su Tallafa Wa Talakawa Tare Da Inganta Haɗin Kai
“Kula da Lafiyar Nasir El-Rufai lamari ne mai matukar damuwa ga iyalansa, abokansa, da abokan aikinsa,” in ji Atiku.
“‘Yan Nijeriya na bin Gwamnatin Tarayya bashin bayanin halin da ake ciki. Dole ne ta fayyace a fili wacce hukuma ce ke tsare da shi, Hukumar EFCC ce, ko Hukumar ICPC ce, ko kuma Hukumar DSS, ko wata hukumar tsaro ce ta daban.”
Atiku ya yi gargadin cewa, nuƙu-nuƙun da ake yi game da tsare El-Rufai, jama’a za su iya yi wa lamarin mummunan zato kuma hakan ka iya lalata aminci ga tsarin shari’a.
[ad_2]
Source link