El-Rufa’i ya buƙaci kotu ta yi watsi da tuhumar da DSS ta yi masa

[ad_1]



Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya buƙaci Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta yi watsi da tuhumar da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta shigar a kansa.

Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da mai magana da yawunsa, Muyiwa Adekeye ya fitar wannan Talatar.

El-Rufa’i wanda yake iƙirarin tuhumar a matsayin maras tushe, ya ce ta saɓa wa kundin tsarin mulki sannan kuma tana cin zarafin tsarin shari’a.

A wata ƙara da ya shigar a gaban Babbar Kotun Tarayya, El-Rufai ya ƙalubalanci tuhumar mai lamba FHC/ABJ/CR/99/2026 wadda take ɗauke da kwanan watan 16 ga Fabrairu, 2026.

Aminiya ta ruwaito cewa an tsara za a fara sauraron shari’ar ce a ranar 25 ga Fabrairu, 2026, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Joyce Abdulmalik.

Sai dai a takardar da ya gabatar, El-Rufai ya nemi kotun ta yi watsi ko ta soke tuhumar, yana mai cewa ba ta bayyana wani laifi da doka ta sani ba, sannan ba ta gina wata hujja a zargin da take yi masa ba.

Bugu da ƙari, tsohon gwamnan ya nemi kotu ta tilasta wa DSS biyansa diyyar kuɗi har naira biliyan 2, yana zargin hukumar ta hannun lauyoyin da ke gabatar da ƙara, da amfani da tsarin shari’a ba bisa ƙa’ida ba domin tsangwama, tozartawa da cin mutuncinsa a idon jama’a.

Takardun kotu sun nuna cewa El-Rufai ya gabatar da dalilai 17 da ke neman a soke tuhumar.

Har ila yau, tawagarsa lauyoyinsa ta sanar da Darakta Janar na DSS game da ƙarar cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 18 ga Fabrairu, tare da bayyana sunayen lauyoyin da ke wakiltarsa.

Daga cikin dalilan da aka jero akwai: rashin sahihancin tuhumar a kundin tsarin mulki, rashin hujjoji kan zargin da ake yi masa, ambaton laifuka da doka ba ta sani ba, rashin cancantar masu gabatar da ƙara, ruɗani a tuhuma, rashin shaidu, mummunar niyya, tsangama ta siyasa da kuma cin zarafin tsarin shari’a.

El-Rufai ya kuma ce ana take masa haƙƙoƙinsa na ɗan Adam a waɗanda aka tanada a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, ciki har da ƙa’idar rashin ɗora wa mutum laifi har sai an tabbatar, haƙƙin ƙin tilasta kai shaidar kanka, wajabcin fayyace laifuka a rubuce a doka, da kuma haƙƙin faɗar albarkacin baki.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *