Ana ci gaba da yi wa DSS matsin lambar sakin Walida

[ad_1]



Ƙungiyoyin kare haƙƙin mata da yara sun ƙara matsa lamba ga Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da ta gaggauta sakin matashiyar nan Walida Abdulhadi, wadda ake zargin wani jami’inta, Ifeanyi Onyewuenyi, da sacewa da kuma aikata lalata da ita.

Batun matashiyar na ci gaba da ɗaukar hankali a Najeriya tun bayan da wasu gungun lauyoyi suka shigar da ƙara suna zargin wani jam’in hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (DSS) da laifin “sacewa da yin lalata da kuma sauya mata addini.”

Walida ta ɓace tun shekarar 2023, lokacin da take ‘yar shekara 16 tun tana ’yar aji 2 a babbar sakandire, amma a watan Disambar 2025 ne mahaifinta ya samu labarin cewa tana Abuja tare da jami’in DSS ɗin, har ta haifa masa jariri.

Tun watan Janairun da ya gabata ne dai DSS ta maƙale kan kujerar naƙi duk da umarnin da wata Kotun Majistire a Jigawa ta bayan tana neman sakinta da kuma gurfanar da jami’in.

DSS ɗin ta ce ta nemi a soke umarnin kotun, tana mai cewa tana riƙe da Walida ne ƙarƙashin “kariya ta musamman”, lamarin da ya ƙara tayar da ƙura a tsakanin jama’a da ƙungiyoyin farar hula.

A wani taron manema labarai da suka yi a Abuja, wata haɗaka ƙarƙashin sunan Concern Coalition for Walida Abdulhadi, wadda ta haɗa da FOMWAN da Women in Da’awah, ta yi gargaɗin cewa DSS ba za ta iya zama mai bincike da mai kare kanta a lokaci guda ba.

Mai magana da yawun ƙungiyoyin, Ustaz Yunus Salahudeen, ya ce dole ne a bar bincike mai zaman kansa ya gudana, yana mai cewa ƙoƙarin sauya shekarun Walida daga 16 zuwa 22 ba tare da hujjoji ba na iya lalata amincewar jama’a.

Ya jaddada cewa bambancin shekarun yana da muhimmanci a doka, musamman kan kariyar yara.

Haka kuma, wani lauya mai rajin kare haƙƙin bil’adama, Barista Hamza Nuhu Dantani, ya aika wa DSS wasiƙa yana zargin ta da ƙoƙarin rufe gaskiya.

Ya buƙaci a miƙa Walida ga iyayenta ko halastattun masu kula da ita, tare da miƙa binciken ga wata hukuma mai zaman kanta, bisa la’akari da dokokin kare haƙƙin yara na Najeriya da na Majalisar Ɗinkin Duniya.

A shekarar 2008 aka haifi Walida — Mahaifinta

Tun da farko, a wata hira da ya yi da Aminiya, mahaifin Walida, Malam Abdul-Hadi Ibrahim, ya ce abin da ya fi ba shi mamaki a ganawarsa da jami’an DSS shi ne iƙirarin da suka yi cewa an haifi ’yarsa ce a shekarar 2004.

Ya ce, “Na auri mahaifiyarta a 2007, kuma aka haife ta a 2008. Wannan yana nufin tana da shekara 16 a lokacin da aka sace ta, kuma yanzu tana da 18. Wataƙila suna son na mutu saboda baƙin ciki kamar mahaifiyarta.

“Har sun ce zan kashe ta idan ta dawo wurina saboda wai ta sauya addini. Amma ta yaya uba zai kashe ’yar da ya sha wahala yana rainonta?

“Ni Musulmi ne, kuma Allah Ya haramta kashe rai. Me ya sa zan kashe ’yar da ta ɓace tsawon shekaru biyu, alhalin ban san irin azabar da ta sha ba a wannan lokaci,” in ji shi.

Mahaifin ya kuma yi kira ga Gwamnan Jihar Jigawa da ya shiga tsakani, yana mai cewa, “Ina roƙon gwamnan Jigawa ya taimaka min, domin wannan wulaƙancin ba ni kaɗai ya shafa ba, ya shafi ɗaukacin al’ummar Musulmi.”

A wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na DSS, Favour Dozie, ya sanyawa hannu, an ce kotu za ta saurari shari’ar nan ba da jimawa ba.

Haka kuma, a wata hira da Aminiya a ƙarshen makon jiya, DSS ta ce tana riƙe da Walida ne a matsayin ƙarƙashin “kulawa ta musamman”.

Sai dai bayan ƙarin kiraye-kirayen da ake yi na sakin Walida, Aminiya ta sake tuntuɓar DSS domin jin martaninta, amma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto haƙar ba ta cimma ruwa ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *