Shugaba Tinubu Ya Haɗa Taron Shan Ruwa, Ya Bukaci Haɗin Kai Daga Gwamnoni
[ad_1]
Shugaban ƙasa Ahmed Boka Tinubu ya gode wa Allah da ya ba su damar shaida wani Ramadan, yana mai cewa lokaci ne na ladabi, da haƙuri, da sadaukarwa da soyayya. Ya lura cewa azumin Ramadan ya zo daidai da na Kiristoci, lamarin da ya ce darasi ne na haɗin kai da juriya tsakanin addinai.
Ya buƙaci gwamnonin su rungumi juna da haƙuri tare da ba matasa dama su numfasa a cikin tsarin mulki. Haka kuma ya yaba da ci gaban da jihohi suka samu, yana mai cewa alamu na nuna ana fita daga ƙalubalen tattalin arziƙi.
- Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 6
- Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Ƙaddamar Da Tallafin Abincin Azumi Da Sallah Ga Mutane 16,000
Shugaban ya sake nanata aniyarsa ta ƙarfafa tsaro da bunƙasa ci gaba a matakin ƙasa da ƙasa, tare da roƙon shugabanni su kula da marasa galihu da faɗaɗa damammaki ga jama’a.
Da yake magana da manema labarai, Gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ya bayyana Iftar ɗin a matsayin taron haɗin kan addinai ne, yana mai cewa gwamnonin na aiki tare da shugaban ƙasa domin bunƙasa ƙasa. Liyafar na daga cikin al’adar Tinubu ta karɓar baƙuncin shugabanni a watan Ramadan.
[ad_2]
Source link