Ya Kamata A Aiwatar Da Sakamakon Taron Kolin Tianjin Don Inganta Kungiyar SCO
[ad_1]
Kafofin yada labarai na duniya sun mayar da hankali kan taron majalisar shugabannin gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar Shanghai SCO na 24 da aka gudanar kwanan nan a birnin Moscow na kasar Rasha. Firaministan gwamnatin kasar Sin Li Qiang ya yi kira ga kungiyar SCO da ta aiwatar da shawarar inganta tsarin shugabancin duniya da Sin ta gabatar, da karfafa kungiyar SCO a fannin hadin kai da aiwatar da harkoki da kuma tasirinta.
Shekaru 24 da suka wuce bayan kafuwar kungiyar SCO, a karkashin jagorancin ruhin Shanghai, an samu habakar abotan kungiyar, da karfafa ingancinta, shi ya sa ma ta zama kungiyar yanki mafi girma a duniya, wadda ta kiyaye muradun kasashe mambobin kungiyar, ta kuma inganta zaman lafiya da ci gaban duniya.
Yayin da take ci gaba da samun bunkasa, kungiyar SCO tana kara taka rawar gani a harkokin duniya, inda ta fito da wata sabuwar hanya dake hada kowa a cikinta, wanda hakan ya ba da misali ga samun ingantaccen tsarin shugabancin duniya.
A kan sabon tafarkin ci gaba, ya kamata a yi amfani da zarafin tabbatar da shawarar inganta tsarin shugabancin duniya, don samar wa SCO wata kyakkaywar makoma mai hadin kai da yin hakuri da juna da samun dorewa da kuma wadata. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link