Kano Pillars Ta Fice Daga Jan Layi Bayan Doke El-Kanemi Warriors

[ad_1]

Kano Pillars ta samu muhimmiyar nasara a Mako na 27 na Gasar Firimiya ta Nijeriya bayan ta doke El-Kanemi Warriors da ci 3-0 a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata, Kano. Nasarar ta sa ƙungiyar ta fice daga jan layi, inda ta koma matsayi na 15 a teburin gasar da maki 32, tana ƙara samun ƙwarin gwuiwar tsira daga faɗa wa gasar ’yan dagaji.

A sauran wasannin ranar Lahadi, Ikorodu City ta ci gaba da jan ragamar teburin da maki 45 duk da canjaras 1-1 da Bayelsa United.

  • Kano Pillars Ta Ƙare Zagayen Farko Na Gasar Firimiyar Nijeriya A Jan Layi
  • Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25

Haka kuma, Rangers International da ke matsayi na biyu ta tashi kunnen doki da Katsina United, yayin da Abia Warriors ta doke Kwara United da ci 1-0.

A wani wasa kuma, Kun Khalifa ta samu nasara da ci 2-0 a kan Niger Tornadoes, lamarin da ya ƙara ɗaukar zafi a fafatawar saman teburin gasar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *