Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Soke Harajin Da Ta Kakaba Bayan Hukuncin Kotun Kolin Kasar

[ad_1]

A yau Litinin, kasar Sin ta yi kira ga Amurka ta soke matakan harajin da ta kakaba wa abokanta na ciniki, bayan kotun kolin Amurkar ta yanke hukunci cewa, haraje-harajen da aka kakaba karkashin dokar gaggawa da ta shafi tattalin arziki ta duniya, sun saba doka.

Da yake martani ga manema labarai, wani kakakin ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta Sin, ya ce kasarsa za ta bibiyi matakan haraji na baya-bayan nan da Amurka ta sanya, kuma za ta jajirce wajen kare halaltattun hakkoki da muradunta. Ma’aikatar ta kuma bukaci Amurka ta soke karin harajin da ta kakaba wa abokanta na cinikayya.

A ranar Jumma’ar da ta gabata ne, 2 bisa 3 na alkalan kotun kolin Amurka suka yanke hukunci cewa, harajin da shugaba Donald Trump ya kakaba wa kasashen duniya karkashin dokar gaggawa da ta shafi tattalin arziki ta duniya (IEEPA), sun saba doka. Alkalai mafiya rinjaye sun ce dokar ba ta ba shugaban ikon kakaba haraji kan kayayyakin da ke shiga kasar ba. (FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *