Abubuwan Da Za Su Taimaka Wa Mai Azumi Ya Kasance Cikin Koshin Lafiya
– Ka da mai Azimi ya yi wasa da shan ruwa lokacin bude-baki. Da zarar lokacin bude-baki ya yi, ya gaggauta shan ruwa kafin ya kai ga cin abinci, sannan ya kamata ya kula; ka da ya take cikinsa da ruwa ta yadda cikin nasa zai kulle; har ta kai shi ga yin amai.
– Ana bukatar mai Azimi ya ci nau’ikan abinci iri daban-daban bayan shan ruwa, dalili kuwa; jikinsa na bukatar abinci mai kyau, wanda zai maye gurbin abin da ya rasa sakamakon wannan Azimi da ya yi. Don haka, akwai bukatar cin abinci mai kyau da kayan marmari da sauran abin da ya shafi dangin ganyayyaki, wadanda za su kara masa lafiyar jiki.
– Haka nan, ka da mai Azimi ya rika cin abinci ya na take cikinsa a lokacin shan ruwa. A tsaya a ci abinci a tsanake, ta yadda za a kawar da yunwa ba tare da an yi cin da zai iya cutarwa ba.
– Sannan, a rika dan motsa jiki bayan shan ruwa, duk dai da cewa, ba za a ba da shawarar a rika motsa jiki da safe ko rana ko kuma yamma ba, saboda yanayin kishirwa da ake fama da ita, amma duk da haka; bayan shan ruwa ka da a lafke, a dan yi kokari a rika dan kai-komo.
– A rika kwantawa ana samun isasshen barci, domin samun kuzari da kuma lafiyar jiki baki-daya.
– Har ila yau, da yake jiki iri daban-daban ne, idan ka jarraba wadannan shawarwari da muka bayar ka ji jikinka bai yi maka yadda kake so ba, tun wuri ka dakata kar ka ci gaba, kana iya samun likitanka; ya ba ka shawara a kan abin da ya fi dacewa da kai.
Haka zalika, ka da a manta cewa; wannan wata shi ne wanda musulmi suka fi so a rayuwarsu baki-daya; inda suke haduwa da mutane daban-daban su ci abinci tare, masu shi su taimaka wa marasa shi tare da kyautata ibada da kuma kara tsoron Allah a lokaci guda.