Tinubu ya yaba wa Wike kan nasarar APC a zaɓen Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bisa jajircewarsa wadda ya ce ita ce silar nasarorin da jam’iyyar APC ta samu a zaɓen da aka gudanar a Abuja.
A ranar Asabar ce Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomi shida na Babban Birnin Tarayya, tare da zaɓukan cike gurbi a mazaɓun Ahoada East II da Khana II a Jihar Ribas, da kuma Kano Municipal da Ungogo a Jihar Kano.
Jam’iyyar APC mai mulki ta samu gagarumar nasara, inda ta lashe mafi yawan kujerun da aka fafata a kansu.
Cikin wata sanarwar da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce Shugaba Tinubu ya taya waɗanda suka yi nasara murna.
Sanawar ta ce shugaban ƙasar ya yaba wa INEC, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a zaɓen, bisa rawar da suka taka wadda ta haifar da nasarar gudanar da zaɓen cikin lumana.
Ya kuma yi kira ga waɗanda aka zaɓa da su yi aiki da ƙanƙantar da kai, kishin ƙasa da jajircewa, tare da kallon amincewar da jama’a suka ba su a matsayin wata babbar amana da ke buƙatar a tsarkake ta.
Shugaba Tinubu ya yaba wa Ministan Abuja, Nyesom Wike duk da kasancewarsa ɗan jam’iyyar PDP, inda ya ce nasarorin da ya samu a Abuja sun haifar wa APC ribar siyasa.
A cewar Onanuga, Shugaban ƙasar ya kuma taya shugabancin APC na ƙasa, da na jihohin Kano da Ribas, da dukkan mambobin jam’iyyar murna kan nasarorin da aka samu a zaɓen.
Ya ƙara da cewa takara da halartar zaɓe na ƙara ƙarfafa dimokuraɗiyya, inda ya buƙaci INEC da ta ci gaba da inganta tsarinta domin samar da zaɓuka masu inganci a nan gaba.