Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe
[ad_1]
Yayin da ake ci gaba da mayar da martani kan fitar da jadawalin hukuma na zaBen 2027 da (INEC) ta yi, matakin ya haifar da gaggawar martani daga jam’iyyun siyasa da dama, inda da yawa daga cikinsu suka bayyana shirinsu na fara tsare-tsare da shirye-shiryen da suka dace da sabon jadawalin.
Dangane da jadawalin, an sanya zaBen Shugaban Kasa da na Majalisaun Tarayya (Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai) a ranar Asabar, 20 ga Fabrairu, 2027, yayin da zaBen gwamna da na ’yan Majalisar Dokokin Jihohi za su gudana a ranar Asabar, 6 ga Maris, 2027.
Hukumar ZaBe ta Kasa mai zaman kanta, (INEC), ta kuma sanar da cewa kamfen din zaBen Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya zai gudana daga ranar 18 ga Nuwamba, 2026, zuwa 19 ga Fabrairu, 2027.
Haka kuma, kamfen din zaBen gwamna da na ’yan Majalisar Dokokin Jihohi zai fara daga ranar 15 ga Disamba, 2026, zuwa 5 ga Maris, 2027, inda za a rufe duk wani kamfen sa’o’i 24 kafin ranar zaBe.
Shugaban Hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su bi jadawalin da aka fitar tare da gudanar da zaBen fidda gwani cikin gaskiya da adalci.
Ya ce: “Dangane da jadawalin da aka amince da shi da kuma Tsarin Ayyuka, za a gudanar da zaBen fidda gwani na jam’iyyu cikin wa’adin da doka ta tanada.”
“Mika takardun tsayawa takara daga jam’iyyun siyasa zai fara kuma ya rufe ne cikin wa’adin da aka kayyade kamar yadda yake a cikin Jadawalin.
“Kamfen din jam’iyyun siyasa zai fara a ranar da doka ta tanada kuma zai kare sa’o’i 24 kafin ranar zaBe.
“Bari in sake jaddada cewa INEC hukuma ce mai zaman kanta. Muna aiki ne bisa ga Kundin Tsarin Mulki, Dokar ZaBe, da Dokoki da Ka’idojinmu. Za mu ci gaba da gudanar da ayyukanmu cikin adalci, gaskiya da kwarewa ba tare da nuna son kai ba.”
Ya yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da su gudanar da zaBen fidda gwani cikin lumana da gaskiya, su guji tashin hankali da kalaman tunzura jama’a, tare da mutunta dimokuradiyyar cikin gida ta jam’iyyunsu.
Haka kuma ya roki ’yan takara, magoya bayansu da masu kada kuri’a da su nuna halin zaman lafiya a duk tsawon lokacin zaBe.
“Nasara da ingancin ZaBen 2027 alhakin kowa ne. Hukumomin gwamnati, jami’an tsaro, kafafen yada labarai, kungiyoyin farar hula, da ma dukkan ’yan Nijeriya dole ne su taka rawar da ta dace a nasu Bangaren.”
“Yayin da muke fara wannan muhimmin aiki na kasa, ina tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa Hukumar ta shirya tsaf kuma ta kuduri aniyar gudanar da zaBe wanda zai nuna cikakken ikon zaBin al’umma.
“A karshe, ina kira ga dukkan jam’iyyun siyasa, ’yan takara da ’yan kasa da su fara shiri domin wannan muhimmin lokaci a dimokuradiyyarmu. Mu hada kai domin tabbatar da cewa tsarin zaBen ya kasance cikin lumana, hada kowa da kowa, kuma ya nuna ainihin muradin jama’ar Nijeriya,” in ji shi.
ADC ta bukaci a fayyace yadda za a yi amfani da tsarin tura sakamako ta na’ura kai tsaye.
A martaninta kan wannan ci gaban, ADC ta ce duk da cewa tana maraba da jadawalin zaBe na INEC, jam’iyyar ta roki Hukumar da ta bai wa ’yan Nijeriya tabbaci a fili kan yadda za a gudanar da tura sakamakon zaBe ta hanyar na’ura a ainihin lokacin.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta ce ingancin zaBen ba kawai ya dogara ne ga jadawalin ba, har ma da hanyoyin gudanarwa masu gaskiya da bayyanawa.
Ta yi kira ga INEC da ta fayyace matakan kariya na hana duk wata yaudara, sannan ta roki Majalisar Kasa da ta amince da doka mai karfi wacce za ta kawar da rashin tabbas kan tsarin tura sakamako ta na’ura a ainihin lokacin.
Ya ce, “Muna maraba da fitar da jadawalin da wuri, wanda ke bai wa jam’iyyun siyasa, masu ruwa da tsaki, da ’yan kasa damar samun cikakken bayani domin tsara tsare-tsare na dogon lokaci da shiri na dimokuradiyya.
“Duk da haka, ingancin ZaBen Gabadaya na 2027 ba zai dogara kawai ga dacewar lokaci na jadawalin ba, amma zai dogara ne ga yadda Hukumar za ta nuna jajircewarta wajen gaskiya, amfani da fasaha cikin aminci, da kuma bin ka’idojin doka a duk tsawon lokacin zaBe.
“Abin da ya fi muhimmanci shi ne batun tura sakamakon zaBe ta na’ura a ainihin lokacin. Duk da cewa Hukumar ta nuna cewa za ta gudanar da aiki ne bisa ga dokar da ta tanada, Dokar ZaBe ta yanzu har yanzu tana bai wa Hukuma ’yancin zaBi a wasu muhimman hanyoyi wanda ke shafar amincewar jama’a kai tsaye.”
A cikin tattaunawarsa da manema labarai kwanan nan, shugaban INEC ya amince da cewa Hukumar na da karfin fasaha don amfani da tsarin tura sakamakon zabe ta na’ura, sannan ya tabbatar da cewa Hukumar za ta ci gaba da amfani da fasaha wajen gudanar da zabe.
Jam’iyyar ADC ta roki INEC da ta bai wa ’yan Nijeriya cikakken bayani cikin lokaci da kuma a fili kan shirinta na karBar tsarin tura sakamako ta na’ura a ainihin lokacin idan an yi gyare-gyaren doka da suka dace.
“Baya ga haka, Hukumar ya kamata ta fayyace matakan tsaro da za a dauka, na hannu da na na’ura, domin tabbatar da ingancin sarrafa sakamakon zaBe da kuma hana faruwar irin matsalolin da suka shafi zaBuka na wasu lokuta da suka gabata.”
“Jam’iyyar ADC ta sake jaddada kiran ta ga Majalisar Kasa da ta hanzarta amincewa da doka mai karfi wacce za ta kawar da rashin tabbas kan tura sakamakon zaBe ta na’ura, tare da karfafa tsarin doka don gudanar da zaBe cikin gaskiya.
“’Yan Nijeriya sun nuna sau da yawa cewa suna shirye su kare tsarkin kuri’un su. Abin da ake bukata yanzu shi ne Hukumar ZaBe ta daidaita wannan fadakarwar dan kasa da cikakken bayani na hukuma, gaskiya a ayyuka, da kwarewar gudanarwa,” in ji sanarwar.”
Jam’iyyar ta kara da cewa, a matsayin ta na jam’iyya mai kwazo wajen zurfafa dimokuradiyya da gudanar da zaBe cikin gaskiya, ADC za ta ci gaba da yin mu’amala mai ma’ana da INEC, Majalisar Kasa, da duk masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa zaBen 2027 ya nuna ainihin muradin ’yan Nijeriya.
PDP da Jam’iyyar Labour Sun Bayyana Ra’ayinsu
Yayin da rikicin shari’a a cikin PDP da Labour Party ya ki ci ya ki cinyewa, Bangarorin da ke yaki a cikin wadannan jam’iyyun sun nuna matakai daban-daban na kwarin gwiwa a gaban zaBe bisa jadawalin da aka fitar.
Yayin da reshen PDP na Kabiru Tanimu Turaki ke nuna taka-tsantsan kan tabbacin INEC na gudanar da zaBe cikin gaskiya da adalci, kwamitin rikon kasa na kasa wanda ministan FCT, Nyesom Wike, ke goyon baya, ya fi nuna kwarin gwiwa kan shirinsu na gudanar da zaBen.
Sakataren yada labaran PDP na kasa mai goyon bayan Turaki, Kwamared Ini Ememobong, ya shaida wa LEADERSHIP Weekend cewa jam’iyyar ta shirya tsaf don zaBe matukar INEC ta cika alkawarin da ta dauka.
Ya ce, “Kowane lokaci da INEC ta shirya don zaBe, PDP ma za ta shirya, muddin za a iya tabbatar da gudanar da zaBe cikin gaskiya, adalci, da aminci.”
Haka kuma, kwamitin rikon kasa na PDP ya ce jam’iyyar ta shirya tsaf don cika dukkan sharudan doka da na ka’ida a cikin wa’adin da aka tanada.
Sakataren yada labarai na kasa na kwamitin rikon na PDP, Hon. Jungudo Haruna Mohammed, ya tabbatar wa mambobin jam’iyyar, musamman wadanda ke da niyyar tsayawa takara a ofisoshin zaBe, cewa duk rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar da kuma shari’o’in da ke jiran hukunci ana bin su sosai, kuma ana sa ran za a warware su kafin wa’adin da aka ba jam’iyyun siyasa don gudanar da zaBen fidda gwani ya kare.
Mohammed ya kara rokon duk masu sha’awar tsayawa takara da su kasance cikin nutsuwa, mayar da hankali, shiri, sannan su bi umarnin da manayan shugabannin jam’iyyarsu za su bayar.
A wata tattaunawa da LEADERSHIP Weekend, daraktan zartarwa na Yiaga Africa, Samson Itodo, ya ce: “Ina maraba da fitar da jadawalin. A cikin ’yan makonnin da suka gabata, mun nuna damuwa akai-akai kan jinkirin kammala gyare-gyaren Dokar ZaBe da tasirinsa ga fitar da jadawalin zaBe.
“Ina yaba wa INEC kan amsa wadannan damuwonin da kuma fitar da jadawalin ba tare da wani jinkiri ba.”
Ya ce wannan sanarwa ta bayar da cikakken bayani da tabbaci da ake bukata domin fara shiri da gaskiya, duk da haka, ya lura cewa fitar da jadawalin mataki ne na farko a cikin dogon lokacin gudanar da zaBe.
Itodo ya ce ingancin ZaBen 2027 a karshe zai dogara ne kan cikakken aiwatar da Dokar ZaBe da ka’idojin da jagororin INEC, ka’idoji da hanyoyin aiki masu bayyana kan tura sakamakon zaBe ta na’ura da tattara su, da gaskiya a harkokin saye, shirin kayan aiki, da amfani da fasaha.
Ya kara da cewa ingancin zaBen zai kuma dogara ne kan kyakkyawar hadin kai da jami’an tsaro domin tabbatar da yanayi mai lafiya na gudanar da zaBe.
“Yayin da Majalisar Kasa ke kammala amincewa da Dokar Gyaran ZaBe, yana da muhimmanci cewa sakamakon karshe kada ya rage tabbaci da tsari da jadawalin ya riga ya kafa,” in ji Itodo.
A nasu Bangaren, Cibiyar Wayar da Kan Jama’a kan Harkokin Dokoki (CISLAC) da Kungiyar Kula da Canjin Mulki (TMG) sun nuna damuwa kan jinkirin amincewa da Dokar ZaBe da aka gyara, wanda zai iya matsa wa’adin muhimmai kamar rajistar masu jefa kuri’a, zaBen fidda gwani na jam’iyyun siyasa, sanarwar zaBe, da lokacin kamfen.
Auwal Musa Rafsanjani, daraktan zartarwa na CISLAC kuma shugaban TMG, a wata tattaunawa da LEADERSHIP Weekend, ya roki INEC da ta yi aiki kafada da kafada da Majalisar Kasa don tabbatar da cewa dokar ta kammala.
Yayin da yake nuna damuwa kan kamfen din da ake gudanarwa kafin lokaci, ya ce: “’Yan siyasa sun riga sun fara kamfen din da ba na hukuma ba, wanda zai iya karkatar da lokacin kamfen na hukuma kuma ya sanya INEC cikin wahala wajen aiwatar da doka.
“INEC ya kamata ta bayyana a fili hanyoyin aiwatar da doka kuma ta tilasta wa jam’iyyun siyasa bin lokacin kamfen din da doka ta tanada. TMG da CISLAC suna jaddada cewa ingancin zaBe ba kawai yana cikin kayan aiki ba ne, har ma yana cikin gaskiya a tsarin gudanarwa.
Tabbatar da cewa kayan zaBe, lokuta, da tsarin aiwatarwa suna da saukin fahimta ga jama’a zai kara amincewa.”
Hulda da kungiyoyin farar hula (CSOs), kafofin watsa labarai, da kamfen na wayar da kan jama’a ya kamata su kasance wani Bangare na batutuwan gyaran tsarin zaBe baki daya.
“Shi ya sa CISLAC da TMG suka yi kokarin ganin an samu cikakken gyaran tsarin zaBe, wanda ya hada da fasahar tura sakamakon zaBe, hukunci kan aikata laifukan zaBe, da wayar da kan masu jefa kuri’a. Wadannan abubuwa sun fi muhimmanci fiye da jadawalin da INEC ta fitar kawai.
“CISLAC ta nuna cewa INEC dole ne ta kare jama’a daga bayanan karya, ta tabbatar da fahimtar doka, sannan ta fitar da jadawali na hukuma a fili lokacin da ya dace domin daidaita shi da dokar gyaran zaBe da ake aiki a kanta.
“Mun bayar da shawarar cewa shirye-shiryen hukumomi da kuma sadarwar jama’a za su kasance masu muhimmanci don kauce wa kurakuran da aka gani a zaBe-zaBen baya,” in ji Rafsanjani.
An gane cewa shugabancin kasa na jam’iyyar da Sanata Nenadi Usman ke jagoranta zai tantance shirin jam’iyyar don zaBe.
Sakataren yada labarai na kasa na reshen Abure, Obiora Ifoh, ya shaida wa LEADERSHIP Weekend cewa jam’iyyar tana mai da hankali kan shari’arta a Kotun Koli, wacce ke neman soke amincewar kotun kasa da kasa ga reshen da wani.
A martaninsa kan jadawalin INEC, Ifoh, wanda reshensa ke sukar matsayin INEC kan rikicin cikin jam’iyyar, ya ce: “Za su gaya mana lokacin da suka shirya; sannan za mu je kotun koli. Da yardar Allah, idan mun samu hukunci, za mu ci gaba daga duk inda INEC ta so mu ci gaba.”
“Fiye da shekara guda, ofishin jam’iyyar ya fuskanci barazanar kungiyoyi da ke da alaka da gwamnatin Jihar Abia, Nigeria Labour Congress, da wani hadin kan da suka kira ‘Labour Party Stakeholders’,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa reshen jam’iyyar ya shigar da korafi ga Shugaban ‘Yan Sanda na Kasa (IGP), yana zargin jami’an ‘yansanda da “shiga tsakanin Bangarorin tare da Sanata Usman” da kuma taimakawa wajen mamaye ofishin ba bisa ka’ida ba.
[ad_2]
Source link