Binciken CGTN: Karin Haraji Mafi Yawa Ya Haifar Da Gibin Ciniki Mafi Girma Kana Manufar Harajin Trump Ta Wargaje

[ad_1]

A ranar 20 ga watan Fabrairu, agogon kasar, kotun kolin Amurka ta yi watsi da babbar manufar karin haraji ta wa’adi na biyu na shugaba Trump. A halin yanzu, yawan harajin fito da Amurka ta sanya ya kai mataki mafi girma tun daga shekarun 1940. Abin mamaki kuma, gibin cinikin kayayyakin Amurka ya kai dala tiriliyan 1.2409 a bara. Harajin wanda yake mafi yawa da aka kakaba da nufin rage girman gibin ciniki, a maimakon haka ya haifar da gibi mafi girma, kuma gibin na iya ci gaba da karuwa. Wani bincike na jin ra’ayoyin jama’a da kafar CGTN da ke karkashin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice ta gudanar ya nuna cewa kashi 94.7 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyi sun yi imanin cewa manufar harajin da aka sanya a karkashin kudurin “sanya Amurka a gaba da komai” ta wargaje baki daya.

Bayan da aka sanar da hukuncin, Trump ya yi gaggawar rattaba hannu kan wata dokar zartarwa da ta sanya karin haraji na kashi 10 kan duk kayayyakin da ake shigowa da su Amurka na tsawon kwanaki 150, tare da maye gurbin wasu kare-karen haraji na gaggawa da kotun kolin take ganin an yi su ba bisa ka’ida ba. A cikin binciken, kashi 92.9 cikin dari na masu bayyana ra’ayoyi sun ce sauye-sauyen da ake yawan yi kan manufofin harajin Amurka da kuma rashin tabbas dinsu za su kara kawo illa ga tattalin arzikin duniya.

An gudanar da wannan bincike ne a dandalolin CGTN na Turanci, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci, da Rashanci, wanda ya jawo hankulan mutane 10,445 wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24. (Abudlrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *