Gwamnatin Kaduna Ta Raba Tiransfoma 600 Da Fitilun Sola 10,000 A Kananan Hukumomin Jihar
[ad_1]
Ma’aikatar kananan hukumomi ta Jihar Kaduna tare da hadin gwiwar kamfanin samar da wutar lantarki na Kaduna sun kaddamar da rarraba manyan tiransfoma 600 da fitilun tituna mai hasken rana (solar) 10,000 ga dukkanin kananan hukumomi 23 na jihar.
An gudanar da bikin kaddamarwar a fadar gwamnati da jihar, inda manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta.
- Iyayen Marayu 501 Ne Suka Samu Tallafin Abincin Azumi Daga Dan Amo A Kano
- 2027: Za Mu Kare Kuri’unmu, Ba Za Mu Maimaita Kuskuren Abin Da Ya Faru A 2023 Ba – Peter Obi
A jawabinsa, kwamishinan kananan hukumomi, Sadik Mamman Lagos, ya bayyana muhimmancin shirin, yana mai cewa wannan hadin gwiwa ne domin tabbatar da shugabanci mai hada kai da kuma bunkasa yankunan karkara da wadanda ba su da isassun kayayyakin more rayuwa.
Ya kuma bukaci shugabannin kananan hukumomi, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da su dauki nauyin kula da kayayyakin da aka raba tare da kare su daga Barna.
A jawabinsa a wajen taron, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya jaddada cewa wannan shiri wani mataki ne na zahiri domin inganta rayuwar al’ummar jihar.
Ya yaba da kokarin shugabannin kananan hukumomi 23 wajen ganin an aiwatar da shirin cikin nasara, yana mai cewa hakan na nuna kudirin gwamnati na samar da muhimman ayyuka da hidimomi ga al’umma a fadin jihar.
Taron ya nuna aniyar gwamnatin Jihar Kaduna na magance kalubalen da al’umma ke fuskanta tare da tabbatar da shugabanci nagari, gaskiya da rikon amana.
[ad_2]
Source link