2027: Za Mu Kare Kuri’unmu, Ba Za Mu Maimaita Kuskuren Abin Da Ya Faru A 2023 Ba – Peter Obi

[ad_1]

Tsohon dan takarar shugabancin kasa kuma jigon jam’iyyar hadaka ta ADC, Peter Obi, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da daukaci magoya bayansa da su kasance a shirye don kare kuri’unsu a 2027.

Obi ya ce lokacin ya yi da za gyara kuskuren da aka tafka a zaBen 2023 tare da samun sabbin dabaru da za su samar da nasara a zaBen 2027.

Ya bayyana haka ne a Uyo, Jihar Akwa Ibom, yayin da yake gudanar da gangamin jam’iyyar ADC. Wannan ya kasance cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar magoya bayansa, Yunusa Tanko ya sanya hannu a kai.

Tsohon dan takarar shugaban kasa ya yi gargadin cewa abin da ya faru a zaBen shugaban kasa na 2023 ba za a bari ya sake faru a wannan zaBe.

Ya ce, “Ba za mu bari a maimaita abin da ya faru a zaBen 2023 ba.

“A shekarar 2027, ko dai ku kare kuri’un da kyau, ko kuma da ga abin da ba daidai ba. Dole mu shirya duka don kare kuri’unmu.

“Ina ga ‘yan’uwana maza da mata na kungiyarmu da ke a Jihar Akwa Ibom, ina muku fatan alheri da kuma yabo mara misaltuwa.

“Lokaci ya yi da za a dauki wasu darussa daga tsarin aiki da kuma dabaru wadada za su iya kai mu ga nasara.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *