Zaɓen Mazaɓu Na APC A Sakkwato Alama Ce Ta Haɗin Kai
[ad_1]
Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen mazaɓu na jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato, Alhaji Lawali Liman Kaura ya bayyana cewar yadda jam’iyyar ta gudanar da zaben ba tare da wata hayaniya ba ya nuna hadin kan da jam’iyyar ke da shi a jihar.
A tattaunawar sa da manema labarai, Kaura ya ce ya gamsu da yadda zaɓen mazaɓu 244 ya gudana a faɗin jihar.
- Gwamnatin Tarayya Da Gwamnonin APC Sun Ba Da Gudummawar Naira Biliyan 8 Ga ‘Yan Kasuwar Singa
- Rikicin Kabilanci A Jihar Ribas Ya Tayar Da Hankalin Al’umma
Shugaban kwamitin ya ce yadda manbobin jam’iyyar suka nuna halaye nagari a yayin zaɓen ya nuna alamar tambarin jam’iyyar na tsintsiya wanda ke nuna haɗin kai.
A kan wannan ya buƙaci dukkanin manbobin jam’iyyar da su ci gaba da nuna halaye nagari a yayin zaɓen jam’iyyar a matakin ƙananan hukumomi da za a gudanar a ranar Asabar.
[ad_2]
Source link