Boko Haram sun ƙone manyan motoci ɗauke da kifi a Borno

[ad_1]



’Yan ta’addan Boko Haram sun ƙone manyan motoci uku ɗauke da kifi a yankin Mile-40 da ke Ƙaramar Hukumar Magumeri a Jihar Borno.

A cewar wasu direbobi, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na rana ranar Alhamis.

Direbobin suna kan hanyarsu ta kai kifin zuwa Maiduguri lokacin da aka kai musu harin.

Wata majiyar tsaro ta ce: “Mun gode wa Allah duk direbobin sun tsira, amma motoci uku; Peugeot J5 biyu da bas ɗauke da kifi an ƙone su gaba ɗaya.”

Wani direba da ya nemi a sakaya sunansa ya ce: “Mun ajiye motocin muka tsere zuwa cikin daji.

“Mun gode wa Allah mun tsira, amma haka na ga yadda hanyar samun abincina ta ƙone ta zama toka. Muna roƙon gwamnati ta yi wani abu a wannan hanya.

“A baya suna sace mutane su nemi kuɗin fansa, amma yanzu suna yawan tare motoci su kwashe kaya su kuma ƙone su.”

Ya roƙi Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro su tura sojoji hanyar domin kare rayuka da dukiyoyin masu amfani da ita.

Idan za a tuna a ranar 10 ga watan Fabrairu, 2026, ’yan ta’adda suka tare manyan tirela huɗu ɗauke da shanu a kan hanyarsu zuwa Maiduguri daga Monguno, inda suka sace sama da shanu 100 sannan suka ƙone motocin.

A baya ma wasu manyan motoci huɗu ɗauke da wake daga Monguno zuwa Maiduguri an tare su kuma aka ƙone su a Garin Kashim, da ke Ƙaramar Hukumar Guzamala.

Direbobi da dama da ke zirga-zirga a hanyar sun shaida wa wakilinmu cewa rashin jami’an tsaro a kan hanyar na bai wa ’yan ta’adda damar kai hare-hare ba tare da tangarɗa ba.

“Wannan shi ne abin da ke faruwa kullum kuma ba a ɗauki mataki ba. Daga Maiduguri, wuraren binciken sojoji kaɗai da ake da su, su ne a Gajiganna, Gajiram, sabon na Mairari, sannan Monguno.

“Idan gwamnati ba ta ɗauki lamarin da muhimmanci ba, kasuwancin dabbobi da hatsi da ya fara bunƙasa a yankunan zai rushe, domin ba za mu ƙara iya ɗora rayukanmu da motocinmu a kan wannan hanya ba.”

Ya buƙaci jami’an tsaro su inganta tsaro a hanyar kamar yadda aka yi a hanyar Gwoza, inda aka jibge sojoji a wurare daban-daban domin daƙile hare-hare.

“Yawancin masu motocin dakon kaya sun janye motocinsu daga wannan hanya. Abubuwan nan na ci gaba da faruwa amma har yanzu ba a ɗauki wani mataki ba,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *