2027: Waɗanda ke tunanin ba za a zaɓi Tinubu a Arewa ba sun yi kuskure — Ganduje

[ad_1]



Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce duk wanda ke tunanin ba za a sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027  a Arewa ba, yana yin babban kuskure.

Ganduje, ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Juma’a, lokacin da shugabannin matasan Arewa daga jihohi 19 suka kai masa ziyara bayan naɗa shi a matsayin uba na “Northern Nigeria Youth Leaders Forum”.

Ya ce Shugaba Tinubu shi ne wanda ya fi kowa cancanta daga Kudancin Najeriya da zai jagoranci ƙasar nan bayan 2027.

Ganduje ya ce Najeriya ta yi sa’a da samun shugaba wanda cikakken ɗan siyasa ne kuma ya san yadda ake tafiyar da mulki.

Ganduje ya ce: “Dangane da zaɓen 2027, duk waɗanda ke tunanin cewa ba za a zaɓi Tinubu ba sun yin babban kuskure.

“Wannan shi ne karo na farko da Najeriya ta yi sa’a ta samu shugaban ƙasa wanda cikakken ɗan siyasa ne. Siyasa ce rayuwarsa, siyasa ce tarbiyyarsa, domin ya gaskata haɗin kan wannan ƙasa.

“Ya sha wahala a baya, ya yi gudun hijira saboda dimokuraɗiyya ta samu ci gaba a Najeriya. Don haka babu wanda ya fi dacewa a zaɓa a 2027 sama da Bola Ahmed Tinubu.”

Ya ƙara da cewa tun kafin a zaɓi marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, an yi yarjejeniya cewa bayan shekara takwas na mulkinsa, mulki zai koma Kudu.

Ganduje, ya ce Tinubu bai yi shekaru huɗu a kan mulki ba, amma an riga an ga manyan sauye-sauye da gyare-gyaren da ya fara aiwatarwa domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan.

Ya ce: “Asiwaju bai yi shekaru huɗu a kan mulki ba yanzu, amma mun ga matakai da gyare-gyaren da ya ɗauka. Gyare-gyaren da ya gabatar domin inganta ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma a ƙasar nan.”

Dangane da cire tallafin man fetur, Ganduje ya ce Tinubu ya yi abin da sauran shugabanni suka kasa yi.

Ya ce: “Dukkanin ’yan takarar da suka fafata da shi a 2023 sun yi alkawarin cire tallafin mai, hatta gwamnatin da ta gabata ta yi wannan alkawari, amma babu wanda yake da ƙarfin hali ya aiwatar da shi. Sai Asiwaju ne ya yi nasarar cire tallafin.

“Yanzu dukkanin gwamnonin jihohi, ba tare da la’akari da jam’iyyunsu ba, sun yarda suna samun kuɗaɗe masu yawa domin bunƙasa jihohinsu. Bai cire tallafin domin amfanin gwamnonin APC ba, ya cire ne domin amfanin ƙasa baki ɗaya. Don haka wannan shugaba yana ɗaukar matakai da za su inganta tattalin arzikin Najeriya.”

Ganduje ya kuma yaba wa shugabannin matasan Arewa saboda ƙudurinsu na tattara ƙuri’u da kuma tara kuɗaɗe domin sayen fom ɗin takarar Tinubu.

Ya ce: “Babu wata babbar sadaukarwa da ta fi wannan. Kuna bayar da kuɗinku, kuna bayar da tunaninku, kuna bayar da ƙarfinku da lokacinku domin tabbatar da sake zaɓen Asiwaju. Ina godiya ƙwarai da gaske.”

Tun da farko, shugaban ƙungiyar, Murtala Muhammad Gamji, ya bayyana Ganduje a matsayin abin koyi, yana mai cewa a lokacin da yake gwamna, ya taimaka masa sosai wajen zama fitaccen jagoran matasa.

Gamji ya ce: “Mun zo ne mu faɗa maka cewa duk inda ka dosa, nan ma za mu dosa tare da kai. Dukkaninmu mun amince za mu goyi bayan sake zaɓen Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta hanyar wayar da kan dukkanin matasan jihohi 19 na Arewa da kuma tara kuɗaɗe domin sayen fom ɗinsa gabanin zaɓe.

“Dole mu yi haka domin wasu mutane suna yaɗa jita-jitar cewa ba za a sake zaɓen Asiwaju a 2027 a Arewa ba, amma wannan ƙarya ce, domin babu wanda ya tallafa wa matasan Arewa kamar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.”

A yayin taron, ƙungiyar ta kuma naɗa Ganduje a matsayin uba na “Northern Nigeria Youth Leaders Forum”.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *