2027: Datti Baba-Ahmed Ya Ayana Neman Takarar Shugaban Ƙasa

[ad_1]

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Sanata Datti Baba-Ahmed, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar Labour Party ta ƙasa a Abuja.

  • Dangote Ya Janye Ƙarar Da Ya Shigar Da Tsohon Shugaban NMDPRA A ICPC
  • ’Yansanda Sun Ceto Yara 4 A Jihar Nasarawa

Baba-Ahmed ya ce wannan buri nasa ba shi da alaƙa da ficewar Peter Obi daga jam’iyyar, inda ya ƙara da cewa tun kafin zaɓen 2023 yake da sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Ya bayyana cewa ya janye burinsa a 2023 ne domin haɗin kan ƙasa, ta hanyar goyon bayan Peter Obi.

Baba-Ahmed ya ce addini ko ƙabilanci ba za su hana shi tsayawa takara ba, domin kundin tsarin mulkin ƙasa ya bai wa duk wani ɗan Nineriya da ya cancanta damar yin takara.

Ya ƙara da cewa zai bi dukkanin ƙa’idojin jam’iyya da na hukumar zaɓe.

Shugaban jam’iyyar Labour Party, Julius Abure, ya yaba masa kan ci gaba da zama a cikin jam’iyyar, yana mai cewa hakan alama ce ta haɗin kai da ƙarfafa jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *